Shugaba Bola Tinubu ya nada Farfesa Abdullahi Saleh Usman a watan Agustan 2024, sannan Majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin nasa bayan watanni biyu. Ya karɓi jagorancin NAHCON a wani lokaci mai cike da ƙalubale na aiki da kuma kyakkyawan tsammanin alhazai na Najeriya.

KARANTA LABARI MAKAMANCIN WANNAN: Hukumar NAHCON Na Fuskantar Gagarumin Sauyi Karkashin Farfesa Abdullahi Sale – Ibrahim Nagarta

Shekara guda bayan haka, ya samu Hadin kan alhazai, hukumomin jihohi, da abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa ta hanyar sauye-sauyen da suka dawo da inganci da gaskiya a tafiyar da aikin Hajji.

 

Aikin Hajjin 2025 ya fito fili da tsari mai kyau. Karon farko kenan, dukkan alhazai ‘yan Najeriya suka samu biza akan lokaci. Jigilar fiye da alhazai 52,000 ta kammalu cikin nasara kafin jadawalin da aka tsara, haka ma dawo da su gida ya kammalu da wuri fiye da yadda aka zata.

 

Alhazai sun ji daɗin karin walwala da jin daɗi ta hanyar masauki kusa da Harami a Madina, abinci safe da dare a kullum, da kuma ingantaccen sufuri tsakanin wuraren ibada. A Mina da Arafat kuma, an samar da tantuna na zamani da abinci, da kulawar lafiya mafi kyau.

 

Daya daga cikin muhimman abubuwa na tarihi shi ne kaddamar da tashin farko na alhazai daga yankin Kudu maso Gabas, inda mutum 315 suka tashi daga Filin Jirgin Sama na Owerri.

 

Haka kuma, Farfesa Usman ya gana da gwamnoni, shugabannin gargajiya da malamai a dukkanin shiyyoyin kasar nan guda shida, abin da ya ƙarfafa jajircewar hukumar wajen kula da walwalar alhazai.

 

A wani mataki na nuna zumunci tsakanin addinai, Farfesa Abdullahi ya karɓi bakuncin shugaban Hukumar alhazai ta Kiristoci ta Najeriya (NCPC), Bishop Stephen Adegbite, a ofishinsa, inda suka yi alkawarin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin

 

Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya ce NAHCON zata dora kan waɗannan nasarori, tare da alkawarin samar da aikin Hajji mafi inganci a 2026 da masauki mafi kyau da abinci mai gina jiki da harkar kiwon lafiya da sufuri.

 

Masu lura da al’amura sun bayyana cewa shekara ta farko ta Farfesa Usman ta sake daidaita NAHCON don samar da ingantacciyar hidimar alhazai. Ana kuma sa ran ƙarin sauye-sauye da za su ƙara inganta tafiyar aikin Hajjin Najeriya a nan gaba.

 

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version