Gwamnan Jihar Sakkwato, Mai Girma Dakta Ahmad Aliyu Sokoto, ya yi bankwana da rukuni na farko na maniyyatan jihar da za su tafi aikin Hajjin shekarar 2026 zuwa Ƙasar Saudiyya mai tsarki.

 

A cewar Shugaban Sashen Yaɗa Labarai da Sadarwa na Hukumar, Faruku Umar, taron bankwanar wanda ya gudana a Filin Jirgin Sama na Sultan Abubakar III da ke Sakkwato, ya samu halartar Amirul Hajj na Jihar kuma Shugaban Tawagar Gwamnatin Jiha, Ministan Kwadago da Samar da Ayyukan Yi na Ƙasa, Alhaji Muhammad Maigari Dingyadi, Babban Sakataren Hukumar Alhaji Ibrahim Umar JJ, jami’an gwamnati da kuma mambobin gudanarwar Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar.

 

Gwamnan wanda Mataimakinsa, Alhaji Idris Muhammad Gobir, ya wakilta, ya taya maniyyatan murnar kasancewa cikin waɗanda Allah Maɗaukakin Sarki Ya zaɓa domin gudanar da wannan ibada mai tsarki a bana.

 

A jawabin bankwanarsa, Gwamna Ahmad Aliyu ya buƙaci alhazan da su zama jakadu nagari na Jihar Sakkwato da Najeriya ta hanyar nuna ɗa’a, haƙuri da tsoron Allah a tsawon zamansu a ƙasa mai tsarki.

 

Ya kuma shawarce su da su kasance masu bin doka da oda, su mutunta ƙa’idoji da dokokin da aka tsara domin gudanar da aikin Hajji, tare da mayar da hankali wajen yin addu’o’i domin zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban Jihar Sakkwato da Najeriya baki ɗaya.

 

Gwamnan ya ƙara da tabbatar wa alhazan cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da bayar da cikakken goyon baya domin tabbatar da gudanar da aikin Hajji cikin nasara da kwanciyar hankali, tare da yabawa Hukumar Jin Daɗin Alhazan ta Jihar Sakkwato bisa shirye-shiryen da ta yi domin jin daɗi da walwalar alhazan.

 

Ya kuma roƙi Allah Ya ba su kariya da jagora, tare da yi musu fatan tafiya lafiya da kuma nasarar sauke farali.

 

Tun da fari, Amirul Hajj na Hajjin 2026 kuma Ministan Kwadago da Samar da Ayyukan Yi, Alhaji Muhammad Maigari Dingyadi, ya taya maniyyatan murnar samun damar gudanar da aikin Hajji.

 

Ya buƙace su da su kasance masu haɗin kai, haƙuri da fahimtar juna a lokacin gudanar da aikin Hajjin, tare da bin umarnin jami’ai da hukumomin Saudiyya domin samun nasarar aikin.

 

Amirul Hajj ɗin ya kuma roƙi alhazan da su yi addu’o’i sosai domin Jihar Sakkwato, Najeriya da shugabanninta, tare da yi musu fatan tafiya lafiya da Hajji karɓaɓɓe.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version