Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya jaddada kudirin gwamnatinsa na inganta ayyukan Hajji a Najeriya, inda ya bayyana bukatar da ake da ita na samar da ayyuka masu inganci a duniya domin tabbatar da samun ingantaccen  aikin hajji.

Gwamnan ya yi wannan alkawarin ne a lokacin da Shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) Farfesa Abdullahi Usman Saleh da tawagarsa suka kai masa ziyarar ban girma a gidan gwamnati da ke Maiduguri.

 

Zulum ya yaba da kokarin NAHCON wajen gudanar da ayyukan Hajji yadda ya kamata, ya kuma ba da tabbaci ga  hukumar na aniyar gwamnatinsa na bayar da goyon baya ga alhazan Nijeriya baki daya.

Ziyarar dai wani bangare ce na kokarin da sabon shugaban Hukumar ta NAHCON karkashin jagorancin Farfesa Abdullahi Sale ta fara yi wajen kai ganawa da dukkanin masu ruwa da tsaki a Harkokin ayyukan Haji a Najeriya

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version