Gwamnatin jihar Legas ta jaddada kudirinta na tallafawa hukumar alhazai ta kasa NAHCON domin samun nasarar sauke nauyin da aka dora mata.
Mataimakin gwamnan jihar Dakta Kadiri Hamzat ne ya bayar da wannan tabbacin a lokacin da tawagar hukumar NAHCON karkashin jagorancin shugabanta Farfesa Abdullahi Usman suka kai masa ziyarar ban girma a ofishinsa dake Legas.
Dokta Hamzat ya yabawa NAHCON kan kokarin da take yi, ya kuma bukaci hukumar da ta magance muhimman batutuwan da suka hada da rage yawan kwanakin da mahajjata ke yi a kasar Saudiyya, magance kalubalen biza, da inganta tsarin ciyar da abinci a lokacin aikin Hajji. Ya kuma yi addu’o’in samun nasarar gudanar da aikin Hajji a kasar nan.
A nasa jawabin, Farfesa Abdullahi Usman ya bayyana irin ci gaban da Hukumar ta samu a shirye-shiryen aikin Hajjin 2025. Ya bayyana cewa an kammala tantance jiragen, nan ba da dadewa ba za a bayyana kudin aikin Hajji, kuma an yi taro da jami’an jihar don kammala shirye-shirye.
Farfesa Usman ya kuma bayyana shirin samar da Tanti na rukunin “A” a Mina ga jami’an gwamnati da sauran manyan jami’ai, inda ya jaddada kudirin NAHCON na ganin an gudanar da aikin Hajji cikin sauki.