Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Sokoto, ta ce ta kammala shirye-shirye kuma nan ba da jimawa ba za ta umarci dukkan maniyyatan da ke fadin jihar su fara biyan kudin aikin Hajjinsu.
Shugaban Hukumar Aliyu Musa ne ya bayyana haka a lokacin da yake yin jawabi ga ‘yan jaridu kan ayyukan gabanin aikin Hajin 2025 a Sokoto.
Musa ya lura cewa tun daga lokacin aka fara shirye-shiryen share fage na aikin hajjin badi, amma har yanzu hukumar ba ta fara sayar da kujeru ga duk wani maniyyatan jihar ba.
Ya bukaci maniyyatan da su kara hakuri domin hukumar nan ba da dadewa ba za ta umarce su da su fara ajiye kasa da Naira miliyan 8.4 don neman kujera.
“Ya kamata jama’a su ci gaba da hakuri domin hukumar ba ta fara karbar wani kudi daga duk wani maniyyaci mai niyya ba.
“Ina tabbatar muku da cewa babu wani lokaci mai nisa da za mu fara da zarar hukumar ta kammala shirye-shiryen ta na karshe,” in ji shi.
Aliyu Musa ya bayyana cewa ya kamata maniyyata su rika tantance bayanai tare da yin watsi da jita-jita game da fara aikin. Ya bayyana wasu kalubalen da aka fuskanta a lokacin aikin Haji na shekarar da ta gabata, amma za a dauki karin matakai don tabbatar da aikin da ke tafe.
Ya yabawa alhazan jihar Sokoto bisa kyakykyawan dabi’un da suka nuna a aikin Hajjin da ya gabata, tare da bada tabbacin samun nasarar aikin hajjin a shekara mai zuwa.
Musa ya kuma yabawa gwamna Ahmed Aliyu bisa goyon bayan da yake baiwa harkokin addinin musulunci a matsayin daya daga cikin manyan manufofinsa masu kyau guda tara musamman ayyukan Hajji.
“A shekarar da ta gabata, Gwamnan ya bai wa kowane mahajjaci daga jihar Riyal 1,000 na kasar Saudiyya, wanda ya nuna yadda ya jajirce wajen kyautata rayuwarsu,” inji shi.
Shugaban ya kuma nuna jin dadinsa ga gwamnatin Saudiyya bisa goyon bayan da ta bayar wajen ganin an gudanar da aikin Hajjin bana cikin kwanciyar hankali da kwanciyar nustuwa.
Madogara: VON
Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version