Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna (KSPWA) ta kaddamar da shirin wayar da kai ga alhazai, wanda aka fi sani da BITA, domin shirye-shiryen aikin Hajjin shekarar 2026.
An sanarwar da Jami’in hulda da jama’a na Hukumar Ibrahim Datti Makarfi ya fitar, yace an gudanar da bikin kaddamar da shirin ne a ranar Asabar, 3 ga Janairu, 2026, a Cibiyar Karatun Al-Kur’ani ta Kinkinau, Jihar Kaduna.
Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Hukumar, Malam Salihu S. Abubakar, wanda Sakataren Gudanarwa, Malam Baba Rufa’i, ya wakilta, ya bayyana shirin BITA a matsayin muhimmin ginshiƙi a cikin shirye-shiryen aikin Hajjin Hukumar.
A cewarsa, an tsara shirin ne domin ilmantarwa, sanarwa, jagoranci da kuma shirya maniyyata ta fuskar addini, lafiya da kuma harkokin gudanarwa, domin tafiyar ibada zuwa Ƙasar Mai Tsarki.
Ya jaddada cewa jin daɗi da walwalar alhazan Jihar Kaduna shi ne babban abin da gwamnatin yanzu ta sa gaba, tare da tabbatar da cewa Hukumar ta kuduri aniyar samar da Hajji mai tsaro, jin daɗi da cikar ibada ga dukkan alhazai.
Ta hanyar shirin wayar da kai na BITA, za a ilmantar da maniyyata kan:
Dokoki da ibadojin Hajji
Matakan lafiya da tsaro
Dokoki da ƙa’idojin ƙasar Saudiyya
Ladabi, haƙuri da kyakkyawan ɗabi’a
Haɗin kai da zaman lafiya a tsakanin alhazai.
Shugaban ya bayyana cewa alhaji mai ilimi shi ne alhaji mai nasara, yana mai jaddada cewa shirin na da nufin kawar da ruɗani, rage kura-kurai, da tabbatar da bin ƙa’idoji yadda ya kamata.
Hukumar ta kuma bayyana ci gaban da ake samu a aikin sake inganta sansanin alhazan Jihar Kaduna (Hajj Transit Camp) da ke Mando, a matsayin wani babban mataki na ƙara inganta jin daɗin alhazai.
Malam Salihu S. Abubakar ya tabbatar wa al’ummar Jihar Kaduna cewa aikin zai kammala kafin fara ayyukan Hajjin 2026.
Da zarar an kammala, ana sa ran sansanin zai kai matsayin zamani da ƙa’idojin ƙasa da ƙasa, tare da samar da:
Ingantattun masauki
Kyawawan wuraren tsafta
Ingantattun ayyukan lafiya da jin daɗi
Muhalli mai kyau, tsari da sauƙin gudanarwa
Ya ce wannan ci gaba na nuna ƙudurinsu na ci gaba da ɗaga matsayin jin daɗin alhazai da tsarin aikin Hajji a Jihar.
Shugaban ya yi amfani da damar wajen nuna godiya ta musamman ga Mai Girma Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, bisa goyon bayansa mai ɗorewa, hangen nesansa na ci gaba, da jajircewarsa wajen kula da walwalar alhazai.
Ya ce goyon bayan da Gwamnan ke bai wa Hukumar, musamman amincewa da tallafawa aikin sake inganta sansanin Hajji da sauran shirye-shiryen jin daɗi, na nuna salon jagorancinsa na tausayi da sanya jama’a a gaba.
A madadin Kwamitin Hajji na Musamman na Jihar Kaduna, shugabanci da ma’aikatan Hukumar, da kuma dukkan maniyyata, Shugaban ya nuna godiya ta zuciya ɗaya ga Gwamna bisa fifita mutunci, walwala da jin daɗin alhazan Jihar Kaduna.
Ya kuma yi kira ga dukkan maniyyata da su dauki shirin BITA da muhimmanci, su halarci dukkan zaman wayar da kai, su yi tambayoyi inda ya dace, tare da bin dukkan ƙa’idoji da umarnin da za a bayar.
Hukumar ta yaba wa malamai, masu gabatar da shiri, kafafen yaɗa labarai da sauran masu ruwa da tsaki bisa haɗin kai da goyon baya wajen tabbatar da aikin Hajji ba tare da tangarda ba.
.
