Hukumar Alhazai ta Najeriya ta bayyana cewa ba za a samu rangwame ko tallafin gwamnati da aka tanadar don gudanar da aikin Hajji na 2025 ba. Kwamishinan ayyuka na NAHCON, Anofi Elegushi, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin, bayan wata ganawar sirri da masu kamfanonin Jirgin yawo.
A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Fatima Usara ta fitar, Elegushi ya tabbatar da cewa ba za a samu rangwamen kudi ga maniyyatan da suka yi rajista a karkashin hukumar jin dadin Alhazai ta jiha ko ta hannun Ma’aikata ba. Sanarwar ta kara da cewa, “An tabbatar da cewa a aikin Hajjin 2025, ba za a samu wani tallafi daga gwamnati na biyan kudin aikin Hajji ga maniyyata ba.
Wannan yana nufin cewa a halin yanzu farashin canjin sama da N1,600/$1, maniyyatan da aka saba biya a kalla $6,000 kowanne, na iya biyan N10m na aikin 2025. Jaridar PUNCH ta rawaito cewa Gwamnatin Tarayya ta baiwa Hukumar Tallafin Naira Biliyan 90 domin tallafawa maniyyata aikin hajjin 2024.
Yayin da hukumar NAHCON ta kasa kayyade kudin ajiya a aikin Hajjin 2025, wasu jihohi ciki har da babban birnin tarayya Abuja sun sanar da fara saka kudi N8.4m ga maniyyatan da suke da niyya.
Da yake jawabi a wasu batutuwan da ke da nasaba da PTO, Elegushi ya bayyana cewa, maimakon kamfanoni 20 na jirgin yawo masu zaman kansu da za su jagoranci gudanar da tafiyar alhazai, ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya ta rage adadin zuwa goma kacal, tare da gindaya sharuddan rajistar mafi karancin maniyyata 2,000. da za a yi la’akari don amincewar samun visa.
Ya kara da cewa duk maniyyatan da suka je aikin hajjin 2023 za a mayar musu da kudin su Riyal 150 na kasar Saudiyya, amma duk da haka NAHCON na dakon bayanin dawo da kudaden aikin hajjin 2022, sai dai PTO da suka yi sansani a filin 18 a shekarar 2022. “Dukkan Alhazan Najeriya 95,000 da suka yi aikin Hajji a shekarar 2023 daga jihohin biyu da kamfanonin jirgin yawo zaman kansu za su karbi SR150 kowanne (Riyal Saudiyya dari da hamsin)
Ya bayyana cewa tuni NAHCON ta fara aiki don biyan kudaden”. “Game da dawowar 2022, Hukumar har yanzu tana jiran ƙarin cikakkun bayanai, duk da haka, Prince Elegushi ya bayyana cewa bayanan dawo da bayanan sun fito ne kawai ga PTOs waɗanda suka yi sansani a Ofishin Field 18 a 2022. Za su karɓi SR62,602 (dubu sittin da biyu) tare.
Sanarwar ta kara da cewa Riyal Saudiyya dubu dari shida da biyu) a matsayin mayar da kudin ciyar da abinci mara kyau a cikin Masha’ir.
Kwamishinan ya kuma fayyace cewa sabanin ikirarin da kamfanonin ke yi na cewa NAHCON na bin PTOs Naira biliyan 17 daga asusun ajiyar Hajji na shekarar 2024 na N25m, hukumar ta samu Naira biliyan 2, miliyan 750 kacal daga kamfanoni 110 da suka yi rajistar aikin Hajjin 2024. Ya ce kudaden sun hada da an karkatar da naira biliyan 1, miliyan 250 daga shekarar da ta gabata. Daga cikin adadin, kamfanoni 30 ne suka nemi a mayar da kudaden da suka kai N750m da aka biya, yayin da kudaden da hukumar ke hannun hukumar da ba a tantance ba ya kai N750m.