Daraktan Gudanarwa na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa, ya kaddamar da fara aikin allurar rigakafi da duba lafiyar maza da mata Alhazan jihar.
Karanta Labari makamancin wannan: Hajj 2025: Hukumar Alhazai Ta Kano Ta fara Aikin Samar Da Biza Ga Maniyyata
Alhaji Lamin Rabi’u ya jaddada cewa wannan aikin na daga cikin muhimman shirye-shiryen aikin Hajji, wanda nufinsa shi ne tantance matsayin lafiyar kowanne Alhaji da ke shirin tafiya. Ya bukaci Alhazai su kiyaye jadawalin da aka fitar bisa tsarin Kananan Hukumomin su, sannan kuma ya umarci dukkan masu kula da tabbatar da cewa ba a bar kowa a baya ba.
A nasa jawabin, Shugaban Kwamitin Daraktoci na Hukumar, Alhaji Yusif Lawan, ya bayyana cewa sunzo wannan Asibitine dake sansanin Alhazai domin karɓar allurar rigakafi tare da sauran mambobin kwamitin da ma’aikata, wani yunkuri ne na nuna cewa aikin lafiyar yana da muhimmanci kuma ba shi da matsala.
Ya yabawa ƙoƙarin ma’aikatan lafiya, inda ya nuna jin dadinsa bisa jajircewar su da ƙwarewar su a aikin.
A wajen bikin, Ko’odinatan Kula da Lafiya ta Hukumar, Hajiya Hindatu Muktar, ta tabbatar da cewa an tanadi dukkan abin da ya kamata domin tabbatar da cewa kowanne Alhaji ya samu cikakken kulawar lafiya da ta dace.
Haka kuma ta nuna godiyarta ga Darakta Janar bisa gyaran da aka yi wa Asibitin sansanin Hajji da kuma samar da kayayyakin aikin lafiya domin amfanin Alhazai.
Darakta Janar tare da tawagarsa sun kai ziyara zuwa wurare da dama, ciki har da Port Health Services domin tabbatar da fitar kati na Yellow Card ga Alhazai, da kuma Asibitin sansanin Alhazai domin duba yadda aikin allurar rigakafi da duba lafiya ke gudana. Sannan sun kai ziyarar ta’aziyya ga jami’an kula da Aikin Hajji na karamar hukumar Nasarawa bisa rasuwar mahaifin ɗaya daga cikinsu.