Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Darakta Janar, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa, tare da Shugaban Kwamitin Daraktoci, Alhaji Yusuf Lawan, ta fara wata ziyara ta hukuma domin duba shirye-shiryen aikin Hajji a Ƙasar Saudiyya.
A sanarwar da Jami’in hulda da jama’a na Hukumar, Sulaiman Abdullahi Dederi ya sanyawa hannu, tace a yayin ziyarar, shugabannin Hukumar tare da manyan jami’an gudanarwa sun kai ziyarar girmamawa da ta aiki ga Shugaban Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman, a Ofishin Ummuljud da ke Makkah.
Ziyarar ta kuma haɗa da cikakken bincike kan masauƙan alhazai a Makkah, da nufin tabbatar da walwala, jin daɗi da tsaron alhazan Jihar Kano a lokacin aikin Hajji.
Wannan bincike wani ɓangare ne na ƙudurin Hukumar na tabbatar da ingantaccen bayar da hidima da kuma inganta ƙwarewar aikin Hajji ga alhazan Kano.
A yayin ganawar, an tattauna hanyoyin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano da NAHCON, tare da duba muhimman batutuwan aiki da suka shafi masauƙi, jigila da walwalar alhazai.
Shugabannin Hukumar sun jaddada aniyarsu ta ci gaba da aiki kafada da kafada da dukkan masu ruwa da tsaki domin tabbatar da aikin Hajji mai sauƙi, ba tare da cikas ba, kuma mai cike da lada ta ruhaniya ga dukkan alhazan Jihar Kano.
