Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da cewa ta kammala karɓar kuɗin aikin Hajjin 2026, bayan cikar wa’adin da aka sanya na biyan kuɗin a ranar Juma’a, 5 ga Disamba, 2025.
A sanarwar da Jami’in hulda da jama’a na Hukumar Sulaiman Abdullahi Dederi ya sanyawa hannu, yace Daraktan Janar na Hukumar, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa, ya bayyana cewa bayan kammala taro tsakanin Hukumar da Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) a Abuja ranar Alhamis da ta gabata, babu wani ƙarin wa’adi da aka amince da shi domin ci gaba da karɓar kuɗin.
Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa ya bayyana hakan ne yayin wani taron tattaunawa da dukkan masu ruwa da tsaki na Hukumar.
Ya ce rufe karɓar kuɗin da wuri ya zama dole sakamakon sabbin ƙa’idoji da hukumomin Saudiyya suka ƙaddamar domin aikin Hajjin 2026.
Sabbin ƙa’idojin sun buƙaci ƙarin tsauraran matakai da kammala shirye-shiryen gudanarwa da wuri domin tabbatar da kyakkyawan tsarin tafiyar da aikin ga maniyyata.
Daraktan Janar din ya kara tabbatar da cewa Hukumar za ta ci gaba da jajircewa wajen samar da ingantattun ayyuka ga dukkan maniyyatan da suka yi rijista, tare da bin dukkan ƙa’idojin kasa da kasa da aka tanada don aikin Hajji.
A nasa jawabin, Shugaban Hukumar, Alhaji Yusif Lawan, ya gode wa duk masu ruwa da tsaki bisa hadin kai da goyon baya.
Ya kuma shawarci maniyyatan da suka cika ka’idoji da su kasance masu haƙuri yayin da Hukumar ke ci gaba da aiwatar da matakai na gaba na shirye-shiryen tashi.
