Wani bincike na musamman da Jaridar  Hajj Chronicles ta gudanar ya gano abin da ake zargin wani shiri ne na cikin gida da nufin lalata ayyukan Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON), bisa ga wasu muhimman takardu da aka fallasa da kuma tattaunawa da wasu manyan jami’an gwamnati da suka san al’amuran da ke faruwa a halin yanzu.

KARANTA LABARI MAKAMANCIN WANNAN : Bincike Ya Nuna Yadda Ake Kirkirar Labaran Karya Don A Bata Sunan Shugaban NAHCON

Wadannan takardu da ake kyautata zaton sun fito ne daga wani rahoton binciken leken asiri na cikin gida sun nuna cewa akwai wata hanyar sadarwa ta wasu mutane a cikin Hukumar da kewaye da ita da ake zargin suna kokarin haifar da rudani a harkokin gudanarwa kafin fara shirin Hajjin 2026.

Takardun na nuni da cewa wannan zargin makircin yana da nufin raunana amincewar jama’a ga shugabancin NAHCON da kuma jefa Fadar Shugaban Kasa cikin mawuyacin hali musamman tsakanin al’ummar Musulmi a Najeriya.

A tsakiyar wannan binciken akwai Shugaban NAHCON, wanda majiyoyi suka bayyana a matsayin mutum mai rikon gaskiya, tsantseni, da shugabanci mai bin umarnin Shugaban Kasa cikin gaskiya da tsari.

A cewar rahoton da aka fallasa, kin amincewarsa da tasirin wasu mutane wajen sarrafa harkokin kudi da tafiyar da hukumar ya haifar da matsin lamba daga wadanda ke neman iko da muhimman bangarorin hukumar.

Wani babban jami’i da ya bukaci a sakaya sunansa saboda tsananin mahimmancin lamarin ya bayyana cewa:

“Kin amincewar Shugaban Hukumar da sabawa ka’idoji ya janyo kokarin kirkirar matsalolin dagula aikinsa.”

Babban abin da rahoton ya bankado shi ne sauyin tsarin da aka yi kwanan nan, inda kulawar NAHCON ta koma daga Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF) zuwa Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa. Tun bayan wannan sauyi, masu ruwa da tsaki sun ruwaito karuwar karya ka’idojin aiki, ciki har da yadda wasu kananan jami’ai ke wucewa shugaban kai tsaye suna mikawa manyan ofisoshi bayanan sirri ba tare da izini ba.

Masana sun gargadi cewa irin wadannan dabi’u, idan ba a magance su da gaggawa ba, na iya rusa tsarin jagoranci a cikin Hukumar, su takaita yanke shawara, su kuma kawo tsaiko wajen shirin gudanar da Hajjin bana.

Masu fahimtar bayanan leken asiri sun yi gargadin cewa duk wani yunkuri na tayar da hankalin NAHCON zai iya haifar da mummunan tasiri ga kasa baki daya.

Yayin da aikin Hajin 2026 ke dada karatowa, duk wata matsala ko tsaiko a shiri na iya janyo fushin jama’a musamman saboda mahimmancin addini da siyasa da ke tattare da Hajj a Najeriya.

A tarihi, duk wata gazawa a manyan cibiyoyin hidimar jama’a kan janyo wa Shugaban Kasa suka da zargi.

Masana sun yi nuni da cewa matsala a tafiyar da al’amuran Hajj na iya rikidewa zuwa matsalar siyasa da zamantakewa.

Rahoton da aka fallasa ya ba da shawarar a yi nazari cikin gaggawa kan tsarin kulawar NAHCON.

Shawarwarin da aka bayar sun haɗa da mayar da hukumar ƙarƙashin ofishin Sakataren gwamnatin tarayya, ko kuma a mika Hukumar Kiristoci zuwa Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa domin daidaito.

Manyan jami’an da Hajj Chronicles ta tattauna da su sun jaddada cewa gaggawar daukar mataki na da muhimmanci don kaucewa lalata suna, tabarbarewar tsarin aiki, ko tsaikon da zai iya shafar shirin Hajjin shekara mai zuwa.

Hajj Chronicles za ta ci gaba da bibiyar lamarin tare da neman karin bayani daga hukumomin da abin ya shafa.

A lokacin wallafa wannan rahoto, NAHCON, Ofishin Sakataren Gwamnatin tarayya, da Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa ba su amsa bukatar karin bayani ba.

 

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version