Rukuni na farko na mahajjata 420 daga Jihar Kebbi domin gudanar da aikin Hajji na shekarar 2025 sun tashi daga Filin Jirgin Sama na Sir Ahmadu Bello da ke Birnin Kebbi da yammacin ranar Juma’a ta hanyar jirgi kai tsaye zuwa birnin Madinah a Kasar Saudiyya.
KARANTA LABARI MAKAMANCIN WANNAN: Hukumar NAHCON Ta Mayarwa Alhazan Jahar Kebbi Naira Miliyan 301.56
A cewar Mai Bai wa Gwamnan Jihar Kebbi Shawara na Musamman kan Harkokin Yada Labarai, Yahaya Sarki yace an bai wa dukan mahajjata kudadensu na guzuri a hannunsu, cikin tsari mai kyau da aka tanada domin tafiyar.
Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Umar Abubakar Tafida, wanda ya wakilci Gwamna Nasir Idris, tare da Amirul Hajj na jihar kuma Sarkin Argungu, Alhaji Sama’ila Muhammadu Mera, da Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kebbi, Faruq Aliyu Yaro (Enabo), sun halarci filin jirgin don yi wa mahajjatan bankwana.
A jawabansu daban-daban, sun yaba wa Gwamna Nasir Idris bisa goyon bayansa maras yankewa wanda ya taimaka wajen samun saukin tashi da wuri ta hanyar bayar da tallafin kudi da kayan aiki ga Hukumar Jin Dadin Alhazai.
Amirul Hajj ya tabbatar da cewa an kammala dukkan shirye-shiryen daukar mahajjatan jihar Kebbi guda 3,800 zuwa kasa mai tsarki, ciki har da fitowar fasfo, bizar tafiya da kuma BTA na mahajjata daga kananan hukumomi 21 na jihar.
“Jimillar mahajjata 420, wadanda suka kasu kashi biyu tsakanin maza da mata, ne aka dauka a jirgin farko,” in ji Sarkin Argungu.
Shugaban Hukumar, Faruq Aliyu Yaro, ya bayyana cewa za a ci gaba da jigilar mahajjatan a cikin jirage guda takwas ba tare da wata tangarda ba, har sai an kammala jigilar duka mahajjatan.
Mahajjatan sun yi tafiyarsu ne cikin jirgin saman Flynas Airline mai nau’in Airbus A380-900 series.
Sa hannu:
Yahaya Sarki
Mai Bai wa Gwamnan Jihar Kebbi Shawara na Musamman kan Harkokin Yada Labarai
9/5/2025