Mahukuntan aikin Hajji sun sanar da haramta daukar trolley bags da karin kaya ga alhazan da za su tafi Mina yayin gudanar da Hajjin 2026, inda suka jaddada cewa kowane alhaji zai tafi da jaka guda kacal.
Umarnin na kunshe ne cikin wata takarda da Hukumar Kula da Aikin Hajji ta fitar a Makkah ranar 6 ga watan Mayu, tare da aikawa jami’an da ke kula da alhazai kafin fara jigilar zuwa Mina.
A cewar takardar, ba za a amince da hand-carry bags, trolley bags ko wani karin kaya ba yayin tafiya zuwa Mina, domin rage cunkoso da saukaka gudanar da ayyuka a wurin.
Mahukuntan sun bayyana cewa an dauki matakin ne saboda karancin sararin da ake da shi a sansanonin Mina, inda ake saukar da miliyoyin alhazai a kwanakin aikin Hajji.
Sun kuma gargadi cewa yawan kaya na iya hana zirga-zirga cikin sansanonin tare da haddasa matsaloli yayin daya daga cikin matakan Hajji mafi cunkoso.
Saboda haka, an umurci jami’an da ke kula da alhazai da su gaggauta wayar da kan maniyyata tare da tabbatar da cikakken bin wannan doka ba tare da wani sassauci ba.
Haka kuma, an shawarci alhazai da su bar duk wani kayan da ba dole ba kafin tafiya zuwa Mina domin tabbatar da tafiya cikin tsari da sauki.
