Hukumar Kula da Ayyukan Hajji ta Ƙasa (NAHCON) na sanar da dukkan maniyyatan da ke shirin zuwa aikin Hajjin shekarar 2026 da su kula da ka’idojin cancantar lafiya da aka amince da su.
A sanarwar da Shugabancin Hukumar ya fitar, bisa ƙa’idojin lafiya na ƙasa da ƙasa da sharuddan tsaro na Ƙasar Saudiyya, maniyyatan da aka tabbatar suna da ɗaya daga cikin cututtuka masu zuwa ba za a ba su damar zuwa aikin Hajjin 2026 ba:
Cutar Zuciya
Gazawar Koda
Cutar Sankara mai (Cancer)
Cututtukan Numfashi da ke buƙatar taimakon iskar Oxygen
Cutar Tunanin Ƙwaƙwalwa (Hauka/Psychiatric illness)
Ciki mai haɗari (High-risk pregnancy)
Nakasa mai tsanani
Cututtuka masu yaɗuwa (Infectious diseases)
Cutar Hanta
Za a gudanar da gwajin lafiya na tilas ga dukkan maniyyatan da suka yi rajista kafin a fitar musu da bizar Hajji. Samun shaidar lafiyar jiki sharadi ne na tafiya.
An kafa waɗannan matakai ne domin kare lafiyar maniyyata, tabbatar da gudanar da ibadu cikin tsaro, da kuma samun nasarar aiwatar da aikin Hajji yadda ya kamata.
Domin samun ƙarin bayani da tantancewa, ana shawartar maniyyata da su tuntuɓi Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jiharsu ko kuma Kamfanonin Shirya Tafiyar Hajji da aka amince da su.
Bin wannan sanarwa wajibi ne.
