Masarautar Saudi Arabia ta kaddamar da sabon tsarin yanar gizo na bayar da izinin shiga Makkah, a matsayin wani ɓangare na tsaurara matakan tsaro gabanin Hajjin 2026

 

Wannan sabon tsari, wanda Hukumar Kula da Fasfo ta ƙasa ta bullo da shi, yana bai wa waɗanda suka cancanta damar neman izinin shiga ta intanet ta hanyar dandalin Absher platform da kuma Muqeem portal, ba tare da buƙatar zuwa ofisoshin fasfo ba.

 

A ƙarƙashin wannan tsarin, dandalin Absher Individuals zai kula da aikace-aikacen izini ga wasu rukuni na mutane, da suka haɗa da ‘yan ƙasashen GCC, masu riƙe da izinin zama na musamman, masu zuba jari, iyayen mata na ‘yan ƙasar Saudiyya, ma’aikatan gida, da kuma ‘yan uwa waɗanda ba ‘yan Saudiyya ba.

 

A gefe guda kuma, dandalin Muqeem zai kula da ma’aikatan da ke aiki a cibiyoyi da ke cikin Makkah, da kuma waɗanda aka ɗauka aiki na musamman domin aikin Hajji.

 

Ana fitar da izinin ma’aikatan wucin gadi ta hanyar Muqeem tare da haɗin gwiwar tsarin Tasreeh, wanda shi ne tsarin dijital na bai ɗaya don izinin Hajji.

 

Hukumomi sun bayyana cewa an haɗa wannan tsarin gaba ɗaya da aiki na izinin shiga Makkah domin sauƙaƙa aiki da kuma hanzarta amincewa da aikace-aikace.

 

A halin yanzu, Saudiyya ta fara aiwatar da dokar hana shiga Makkah ba tare da izini ba tun daga ranar Litinin, 13 ga Afrilu, 2026.

 

Hukumar Tsaron Jama’a ta ƙasa ta bayyana cewa ba za a bari baƙin haure su shiga birnin mai tsarki ba idan ba su da ingantaccen izinin aiki a wuraren ibada, ko izinin zama na Makkah, ko kuma takardar izinin Hajji.

Ana sa ran wannan sabon tsarin na intanet zai taimaka wajen daidaita shigar jama’a da kuma ƙarfafa bin doka yayin da Masarautar ke shirin karɓar miliyoyin alhazai domin Hajjin 2026.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version