Yayin da ake kokarin bata masa suna a baya-bayan nan, Shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya ci gaba da jajircewa wajen ganin an tabbatar da gaskiya da rikon amana a ayyukan Hajji. 

 

Da yake mayar da martani game wani labara da wasu bata-gari ke yadawa da nufin bata sunan shugabancin NAHCO, Kodinetan kungiyar tallafawa alhazan Najeriya ta kafafen yada labarai na shiyyar Kano da Jigawa, Nura Ahmad, ya tabbatar da cewa “Babu wani batanci da zai sa shugaban hukumar NAHCON ya kauce daga babbar manufarsa ta tabbatar da gaskiya da rikon amana a ayyukan Hajji.”

 

A makonnin da suka gabata ne dai wasu zarge-zarge da ba su da tushe suka taso, inda aka yi karyar cewa Shugaban Hukumar NAHCON shi daya ya soke kwangilar da Hukumar ta yi da kamfanin dake yi wa alhazai hidima a Saudiyya, wanda hakan zai kawo cikas ga Alhazan Najeriyar a aikin Hajjin 2025.

 

Wannan ikirari dai mutane da yawa sun musanta shi daga hukumar NAHCON da masu ruwa da tsaki a aikin Hajji, wadanda suka tabbatar da cewa duk yarjejeniyoyin suna nan daram, kuma shirye-shiryen aikin hajjin na tafiya yadda ya kamata.

 

Farfesa Usman ya musanta wadannan tuhume-tuhume da kakkausar murya, musamman ikirarin da kungiyar shugabannin hukumomin jin dadin alhazai na jihohi suka yi kan cewa shi kadai ya soke kwangilar masu hidimar ba tare da tuntubarsu ba.

 

Ya kalubalanci wadanda ke wannan zargi da su bayar da kwararan hujjoji da za su tabbatar da ikirarin nasu, inda ya kara da cewa ba a yanke wani muhimmin hukunci dangane da ayyukan Hajji ba tare da tuntubar shugabannin kungiyar ba.

 

“Idan suna da wata hujja, to su gabatar da ita ga jama’a. NAHCON tana gudanar da aiki cikin gaskiya, kuma duk shawarar da aka yanke game da masu yi wa alhazai hidima an yi ne bisa bin ka’ida,” ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da DCL Hausa.

 

Da yake karin haske kan ziyarar aikin da yake ci gaba da yi zuwa Saudiyya, Farfesa Usman ya bayyana cewa ya yi wata ganawa da ma’aikatansa na Makkah, inda suka yi masa bayani kan muhimman batutuwan da suka shafi shirye-shiryen Hajjin bana.

 

“Muna da wani taro da ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya. Mun zo nan don fayyace batutuwa masu cin karo da juna dangane da masu ba da sabis. Ba za mu iya naɗe hannayenmu kawai mu ƙyale ƙoƙarinmu ya zama a banza ba,” Shugaban ya jaddada hakan

 

Shugaban ya kara da tabbatar wa alhazai da masu ruwa da tsaki cewa duk yarjejeniyoyin kwangilar suna nan daram sannan kuma shawarar da NAHCON ta yanke a koda yaushe yana da amfani ga alhazan Najeriya.

 

Ya ci gaba da cewa, “muna mayar da hankali ne kan ganin cewa alhazan Najeriya sun samu ingantattun hidimomi a farashi mai sauki. Ba za mu shagaltu da zarge-zargen da ba su da tushe balle makama ba.”

 

Masu kishin bunkasa walwalar alhazai da suka hada da Kungiyar ‘Yan jaridu masu Tallafawa Alhazan Najeriya (NHMST), sun yi kira ga al’umma da su yi watsi da wannan mummunan labari, suna masu bayyana hakan a matsayin wani yunkuri na masu zagon kasa na haifar da firgici na babu gaira ba dalili a cikin harkar Hajji.

 

“Wadannan labaran karya aikin wasu mutane ne da ke neman yin amfani da tsarin don biyan bukatun kansu,” in ji Kodinetan NHMST na kasa, Ibrahim Abubakar Nagarta, a wata sanarwa da ya fitar kwanan nan.

 

Duk da wannan kalubalen, NAHCON ta ci gaba da jajircewa wajen ganin an gudanar da aikin Hajji mai inganci ga alhazan Najeriya.

 

Hukumar karkashin jagorancin Farfesa Abdullahi Saleh Usman ta baiwa masu ruwa da tsaki tabbacin cewa za a ci gaba da yada bayanai kan aikin Hajjin 2025 ta hanyoyin da aka tabbatar.

 

A yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen gudanar da aikin Hajin 2025, masu ruwa da tsaki sun bukaci hadin kai tare da mai da hankali kan hadafin hadin gwiwa na inganta ayyukan Hajjin Najeriya maimakon barin abubuwan da za su kawo cikas ga ci gabansa.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version