A ci gaba da shirye-shiryen fara karbar kudin ajiya da rijistar maniyyata na shekarar 2025, hukumar jin dadin alhazai ta jihar Katsina ta gudanar da wani taron hadin gwiwa a ranar Talata tare da mambobin hukumar da ma’aikatan gudanarwa.
Taron wanda ya gudana a dakin taro na hukumar, ya mayar da hankali ne kan duba muhimman batutuwan da suka shafi aikin Hajji na shekarar 2024 da kuma bayyana dabarun karbar kudaden ajiyar maniyyata na shekarar 2025 da rajistar maniyyata.
A jawabinsa na maraba shugaban hukumar, Alhaji Kabir Bature Sarkin Alhazai ya yabawa ma’aikatan hukumar da ma’aikatan bisa jajircewarsu wajen gudanar da aikin Hajjin 2024. Ya kuma nuna jindadinsa bisa namijin kokarin da suke yi wajen ganin an samu nasarar ayyukan.
Shi ma Daraktan Zartarwa na hukumar, Alhaji Yunusa Abdullahi Dankama ya yabawa ma’aikata bisa kwazon da suke yi.
Ya bayar da karin haske kan taron da hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta gudanar a Abuja kwanan baya, wanda ya yi bayani kan shirye-shiryen karbar kudaden ajiyar maniyyata da kuma rijistar aikin Hajjin na 2025 mai zuwa.
Alhaji Dankama ya ci gaba da yin kira da a ci gaba da yin hadin gwiwa tsakanin ‘yan kwamitin, gudanarwa, da ma’aikata domin tabbatar da samun nasarar hukumar.
Ya kuma mika godiyarsa ga Gwamnan Jihar Katsina, Mallam Dikko Umar Radda, bisa irin goyon bayan da yake baiwa hukumar.
Babban abin da ya fi daukar hankali a taron, shi ne gabatar da sabon daraktan gudanarwa Malam Nasiru Ladan.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar Badaru Bello Karofi ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar.