Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta bayyana shirin mayar da sama da Naira miliyan 95 ga maniyyata 1,571 da suka yi aikin Hajjin shekarar 2023 hakan  ya shafi ayyukan da ba a yi musu ba a lokacin aikin hajjin.

 

Da yake jawabi yayin ganawa da manema labarai a Dutse a ranar Alhamis din da ta gabata, Darakta Janar na hukumar, Ahmad Labbo, ya bayyana cewa kowane maniyyacin da abin ya shafa zai karbi Naira 61,080 kai tsaye a asusun ajiyarsa na Banki.

 

Labbo ya bayyana cewa, “Jimillar kudaden da za a mayar musu ya kai N95,156,680, wanda za a raba tsakanin mahajjata 1,571. Kowane mutum na da hakkin ya samu N61,080.”

 

Ya kara da cewa jami’an hukumar na shiyyar an dora musu alhakin tattara bayanan asusun Banki na duk wadanda suke da hakkin kudaden domin a samu saukin biyansu kudaden.

 

“A halin yanzu muna tattara bayanan asusu daga maniyyatan da abin ya shafa, kuma da zarar an kammala aikin za a tura musu da kudaden cikin gaggawa,” inji shi.

 

Maido da kuɗaɗen ya nuna jajircewar hukumar na bin diddigi da kuma tabbatar da cewa an yi wa alhazai adalci kan ayyukan da aka biya musu ba yayin gudanar da aikin Hajin na 2023

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version