Hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta gudanar da taro da sakatarorin hukumar jin dadin alhazai ta jiha a karkashin kungiyar shugabannin hukumomin alhazai na jahohi.

Taron dai na da nufin tantance matakin shirye-shiryen hukumar alhazai ta jihar.

A jawabinsa na bude taron, shugaban hukumar NAHCON Farfesa Abdullah Saleh Usman ya tunatar da majalisar cewa aikin Hajji na cikin shiri na karshe kafin a fara aikin Hajjin shekarar 2025.

Ya kuma yi kira ga Jihohin da su kara sanarwa Hukumar NAHCON akan matakin da kowace jiha ta samu a fannin samar da Biza, allurar rigakafi, siyan jakunkuna da sauransu.

A yayin taron, kwamishinan ayyuka, Prince Anofiu Elegushi ya bayyana cewa  an baiwa kamfanin Air Peace alhazai 5,128 daga jihar Abia, Akwa Ibom, Anambra, Sojoji, Bayelsa, Benue, Borno, Cross River Delta, Ebonyi, Edo, Ekiti, Enugu, Imo, Kogi, Ondo, Rivers, da Taraba.

A daya bangaren kuma FlyNas ta ware maniyyata 12,506 daga Babban Birnin Tarayya, (FCT Abuja), Kebbi, Lagos, Ogun, Osun, Sokoto da Zamfara.

FlyNas na kawo jiragen sama guda tara domin gudanar da aikin. Kamfanin Max Air na jigilar alhazai daga jihohin Bauchi, Gombe, Jigawa, Kano, Katsina, Kwara, Oyo da Plateau.

Kamfanin jirgin ya yi alkawarin kawo karshen jigilarsa na alhazai guda 15,203 zuwa 24 ga Mayu. Za a tura jiragen sama guda biyu don gudanar da aikin- B747 mai karfin 400 sai na biyu mai karfin 560. Umza dai an ware mata mahajjata 10,163 daga jihohin Kaduna, Adamawa, Nasarawa, Neja da Yobe. Umza tana tura jiragen B747 mai karfin 477 da B777 mai karfin 310.

An yi lissafin rabon jigilar  alhazai na shekarar 2025 akan jimillar mahajjata 43,000. Kwamishinan tsare-tsare (PRSILS), Farfesa Abubakar Yagawal ya sanar da taron irin shirye-shiryen da Hukumar ta ke da shi ta fuskar asibitocin da aka tanadar a Makkah da Madina, da raba katinan allurar rawaya ga jahohi, sannan a karshe ya tunatar da su kada su sanya mata masu juna biyu aikin Hajji.

Taron ya ci gaba da tattaunawa tare da amincewa da ranar 9 ga Mayu a matsayin ranar kaddamar da jirgin da zai fara tashi da kuma kammala a ranar 24 ga Mayu. 

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version