Dangane da korafe-korafen da aka samu a baya bayan nan da aka sanar da masu kamfanonin jirgin yawo masu zaman kansu guda 10 da aka ba su takardar shedar gudanar da ayyukan Hajji na 2025 a karkashin kamfanoni masu zaman kansu, hukumar na son sanar da jama’a cewa a shirye ta ke ta karbi korafi a hukumance kan duk wani kamfani

 

A sanarwar da mataimakiyar Daraktar harkokin yada labarai da dab’I ta hukumar, Fatima Sanda Usara ta sanyawa hannu, tace Hakan dai ya yi dai-dai da kudurin Shugabancin Farfesa Abdullahi Sale Usman na magance duk wani zarge-zargen da ake yi wa hukuncin da ta yanke cikin adalci ba tare da nuna son kai ba.

 

Don haka, NAHCON ta gayyaci mutane ko kungiyoyi masu sahihan shaidun da ke tabbatar da dalilin da ya sa wasu ko duk kamfanonin da aka ambata ba su cancanta su kasance cikin manyan kamfanonin, da za su gabatar da korafinsu a ranar Juma’a ko kuma kafin ranar Juma’a, 3 ga Janairu 2025.

 

Irin wannan shaida za ta sauƙaƙe. sake duba zabin da kuma sake yin cikakken bincike da zai baiwa Hukumar damar daukar matakin da ya dace idan an tabbatar da zargin.

 

Bisa la’akari da abubuwan da ambata, rubutattun abubuwan da aka gabatar, tare da ingantattun shaidu da ke tabbatar da da’awar sai a aika zuwa ga: “Shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON)”, kuma a gabatar da shi a ko kafin Juma’a, 3 ga Janairu, 2025.

 

Shugaban hukumar ya  bahar da tabbacin cewa duk abubuwan da aka gabatar za a bi duba su ya hanyar da ta cancanta, kuma za a gudanar da duk bincike daidai da kudurin Hukumar na yin adalci.

 

Haka kuma Hukumar ta NAHCON  karkashin jagorancin Farfesa Abdulllhai Sale Usman ta bukaci hadin kai da fahimtar masu ruwa da tsaki da sauran al’umma wajen cimma burin da aka bayyana a baya.

 

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version