Ƙungiyar Association of Hajj Media Support Professionals (AHMSP) ta bibiyi lamari cikin tsanaki da kulawa kan abin takaici da ya faru tsakanin Hukumar Hajji ta Ƙasa ta Najeriya (NAHCON) da wani kamfanin ba da hidimar Alhazai da ke Saudiya, Mashariq Al-Dhahabiyya, dangane da yunƙurin sake duba yarjejeniyar hidima da tuni aka kammala aka kuma rattaba hannu a kanta.

Wannan mataki na iya ɓata kyakkyawan sunan NAHCON tare da haifar da ƙarancin ingancin hidima ga alhazan Najeriya idan aka bari ya samu nasara.

Ana zargin Mashariq Al-Dhahabiyya da haɗa baki da wasu shugabannin Hukumar Jin Daɗin Alhazai na jihohi masu son zuciya, waɗanda ba sa fatan shugabancin NAHCON ko alhazan Najeriya su samu nasarar Hajjin 2026.

An ce sun yi hakan ne ta hanyar wasu dabaru marasa kyau domin rushe shirye-shiryen da tuni aka tanada, musamman yarjejeniyoyin hidimar da aka riga aka sanya hannu a kansu domin alhazan Najeriya a hajjin da ke tafe.

Ƙungiyar ta (Association of Hajj Media Support Professionals) ta bayyana fargaba cewa, idan aka bar wannan mataki na kamfanin Mashariq Al-Dhahabiyya ya ci gaba, zai iya jefa Najeriya cikin haɗarin kasa samun damar halartar aikin hajjin bana, musamman a wannan lokaci da shirye-shiryen Hajjin 2026 suka kai matakin ƙarshe a duniya.

Sai dai, kamar yadda gaskiya ke rinjayar ƙarya da mugunta a koda yaushe, shugabancin NAHCON ya samu nasarar warware matsalar cikin gaggawa da lumana, tare da taimako da saurin tsoma bakin Jakadan Ƙasar Najeriya (Consul) a Saudi Arabiya.

Saboda haka, Ƙungiyar Association of Hajj Media Support Professionals, ta hannun Shugaban na kasa, Ibrahim Abubakar Nagarta, na yabawa da jinjinawa ƙoƙari, hangen nesa da kishin ƙasa da Shugaban NAHCON mai jajircewa, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, tare da Kwamishinoninsa, suka nuna wajen kare haƙƙin alhazan Najeriya da martabar ƙasa baki ɗaya.

Bugu da ƙari, ƙungiyar na sake jaddada cikakken goyon bayanta ba tare da shakka ba ga kyakkyawan aikin da Hukumar Hajji ta Ƙasa ke yi a ƙarƙashin jagorancin Farfesa Abdullahi Saleh Usman, domin tabbatar da cewa Hajjin 2026 ya gudana lafiya, ba tare da tangarda ba, kuma cikin nasara ta kowanne fanni.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version