Daga Suwaiba Ahmed – Shugaban hukumar Alhazai ta kasa NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya amince da nada Alhaji Alidu Shuti a matsayin muqaddaashin Sakataren hukumar.

 

Nadin ya biyo bayan murabus din radin kai da Dr Abdullahi Rabi’u Kwantagora ya yi ranar 6 ga watan Disambar shekara ta 2024.

 

Kafin nadin nasa, Alhaji Alidu Shuti shi ne Daraktan sashan tantancewa da tabbatar da bin qa’idoji a hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON) tun daga shekara ta 2023. Darakta Shuti zai rike wannan mukami na muqaddashin Sakataren hukumar har zuwa lokacin da za’a nada wani sabon Sakataren.

 

Tun daga shekara ta 2007 kawo yanzu, Alhaji Shuti ya rike mukamai da dama a hukumar.

 

Alhaji Shuti dai ya fara aiki a hukumar Alhazai ta kasa tun daga karamin ma’aikaci har ya kai ga matsayi Darakta, hakan ya sa ya zama kwararre a fannin Haji da Umrah. Ya rike Shugaban sahen kula da Kamfanonin jiragen yawo, sai Karamin Mataimakin Darakta a sashen bada Lasisi, sai Mataimakin Darakta a sashen hulda da Jahohi da Yankuna da kuma Mataimakin Shugaban kula da ayyuka a Makkah (2022-2023).

 

Alhaji Alidu Shuti ya yi karatu a fannoni daban daban da suka hada da Digiri na biyu a fannin Ma’aikata da Digiri a fannin Muslimci da kuma difuloma a fannin Jarida. Ya dai kara samun gogewa a harkar Hajji a irin tararrukan karawa juna sani da ya halarta a ciki da wajen Najeriya da suka hada da kasar Birtaniya , Hadaddiyar Daular Larabawa , kasar Saudiyya da dai sauransu.

 

Irin kwarewa da gogewar Alhaji Shuti a fannin Hajji yasa ake ganin zai iya rike kujerar Sakataren hukumar na wucin gadi da zai sa a samu nasarar aikin.

 

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version