Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta samu labarin cewa wasu mutane da ke bayyana kansu a matsayin wakilai na kamfanoni suna amfani da sunan hukumar wajen yin alkawurran da ba su ba da izini ba ga masu samarwa maniyyata masauki da kuma shirye-shiryen ciyar da alhazai a kasar Saudiyya gabanin Hajjin 2025.

 

Wasu daga cikin wadannan mutane har sun tuntubi ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya, da sunan hukuma NAHCON.

 

A nasarwar da mataimakiyar Daraktar hulda da jama’a da dab’I ta hukumar, Fatima Sanda Usara ta fitar, tace Shugaban Hukumar Farfesa Abdullahi Saleh Usman na sanarwa jama’a da dukkanin masu ruwa da tsaki dake ciki da wajen kasar nan cewa, NAHCON ba ta bawa wani mutum ko kungiya ko wakili ikon yin kwangila ko yin wani shiri a madadin Hukumar NAHCON ko dai a Najeriya ko Saudiyya don gudanar da aikin Hajji mai zuwa. . Dukkanin ma’amalar NAHCON a hukumance ana gudanar da su ne ta hanyar ma’aikatanta kawai, kuma dole ne a bi hanyoyin da suka dace.

 

Duk wata yarjejeniya da aka kulla ba tare da amincewar Shugaban hukumar ba kuma ba tare da shigar da ma’aikatan NAHCON da aka nada ba, ba ta da inganci, kuma Hukumar ba za ta amince da ko mutunta irin wadannan kwangilolin ba.

 

A don haka NAHCON na kira ga jama’a  da masu samar da ayyuka na Saudiyya da Najeriya da sauran al’umma da su sanya ido tare da tabbatar da duk wata hulda da Hukumar ta hanyoyin sadarwa a hukumance. Wannan sanarwar na nufin kare masu ruwa da tsaki daga fadawa cikin ayyukan zamba. Hukumar ba za ta dauki alhakin duk wani asarar da aka samu ba saboda yarjejeniyar da ba ta da izini ba.

 

Don ƙarin bayani ko kuma tabbatar da sahihancin duk wata mu’amala da ta shafi NAHCON, tuntuɓi Hukumar a hukumance.

 

 

 

 

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version