Hakan ya faru ne saboda irin kyakkyawan shirin da Gwamnatin Jihar ta yi na shirye-shiryen da ya dace da kuma tsare-tsare masu kyau na aikin Hajjin 2025.
KARANTA LABARI MAKAMANCIN WANNAN; Shugaban NAHCON Ya Sake Jaddada Aniyar Dorewa Kan Daukar Nauyin Gudanar Da Aikin Haji
Sakataren zartarwa na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Neja, Sheikh Muhammad Awwal Aliyu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Jibrin Usman Kodo ya sanyawa hannu domin bayyana bikin fara tashin alhazan
Sakataren zartarwar ya bayyana cewa kamfanin Jirgin Sama na UMZA dake da alhakin jigilar Alhazai a Jiha a ranar Juma’a 9 ga watan Mayu, 2025 zai fara jigilar Alhazan Jihar 2,881 da suka yi rijista.
Ya bayyana cewa hukumar na kan ci gaba, tare da aiki tukuru don ganin an tsara duk wani bangare na tafiyar. A cewarsa, Hukumar ta ci gaba da mai da hankali kan burinta na ganin cewa aikin Hajjin bana ya zama abin tunawa da kuma inganci ga daukacin Alhazan Jihar.
Ya yaba da goyon baya da jajircewar Gwamna Mohammed Umaru Bago wanda ya nuna jagoranci na gaskiya ta kowace fuska.