Mataimakin shugaban kasar Kashim Shettima, bawa ‘yan Najeriya da daukacin al;umar musulmi tabbacin cewa babu wani maniyyacin Najeriya da zai rasa zuwa aikin, kuma za a gudanar da aikin ba tare samun wata matsala ba
Haka kuma, ya umarci Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta dauki dukkan matakan da suka dace don tabbatar da ganin dukkanin maniyyatan Najeriya sun yi aikin Haji ba tare da samun wata matsala ba
Wannan shi ne sakamakon zaman da mataimakin shugaban ya gudanar da shugabannin gudanarwa a ofishinsa dake fadar shugaban kasa ranar litinin
Shettima ya kira taron ne biyo bayan rahoton cewa an samu matsala da kamfanin da zai yi wa algazai hidima mai suna Mashariq Al-Dhahabiah wanda hak ka iya sanyawa a ki yi way an Najeriya
“Ba za mu ƙyale mahajjatan Najeriya rasa zwa aikin hajjin 2025. Aikin hajji zai zama cikin sauki, kuma kowane kalubale za a magance shi da sauri, “Inji Shettima
A don haka sai Mataimakin shugaban kasar ya bawa shugabancin NAHCON umarnin daukar dukkanin matakai wajen kare mraden maniyyatan Najeriya, inda yace ” Ya zama wajibi gat a yi dukkanin abun day a wajaba wajen tabbatar da ganin maniyyatan Najeriya sun samu zuwa Haji ba tare samun wata matsala. Inda yace daga yanzu ya zama dole mu yi wani tsari na musammam domin tafiya ta hanyar da ta fi dacewa don gudanar da Haji cikin nasara”
Tunda farko da yake Magana kan nuna damuwa dangane da batun soke kwangila tare da kamfanin kamfanin Saudiyya, shugaban NAHCON Farfesa Abdullahi Saleh Usman,
Ya kuma yi watsi da zargin da kungiyar shugabannin hukumomin alhazai na jahohi suka yi cewar lamarin zai shafi aikin Hajin