Kungiyar goyon bayan siyasa ta Tinubu Vanguard for 2027 ta ce ta gano wani kamfen na miliyoyin naira da aka kaddamar domin bata sunan shugaban Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Usman.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, kungiyar ta zargi wasu mutane da daukar nauyin hare-haren kafafen yada labarai domin su bata sunan shugaban hukumar tare da kawo cikas ga ayyukan hukumar kafin gudanar da aikin Hajjin 2026.
Kungiyar ta bukaci hukumomin tsaro da su gudanar da bincike kan wannan zargin tare da gurfanar da wadanda ke da hannu a gaban doka.

Shugabar kungiyar, Bisola Abdulkadir, ta bayyana cewa, yunkurin bata sunan shugaban hukumar na da nasaba da siyasa.

Ta ce an yi hakan ne domin kawo tangarda ga shirin hukumar na tabbatar da gudanar da aikin Hajji cikin nasara a Najeriya.

Abdulkadir ta yi gargadin cewa wannan kamfen din a zahiri ana yi ne kan Shugaba Tinubu, inda ta ce wadanda ke daukar nauyin lamarin na kokarin juyar da ra’ayin Arewa kan shugaban kasa ta hanyar tilasta sauke shugaban NAHCON.

Ta ce: “Muna da sahihan bayanai cewa an zuba miliyoyin naira a wani kamfen domin bata sunan shugaban Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) da nufin dakile shirin hukumar na gudanar da shirye-shiryen Hajji.

“Muna kira ga jama’a da su yi watsi da wannan kamfen din na siyasa. Abin da hukumar ke bukata a yanzu shi ne goyon baya, ba cikas ba.

“Irin wannan dabi’ar batawa masu aiki tukuru da kishin kasa suna saboda wasu son zuciya ba za a lamunta da ita ba, kuma ‘yan Najeriya dole su taso su kalubalanci masu daukar nauyinta.

“Gwamnatin Tinubu tana aiki tukuru dare da rana domin samar da nagartaccen mulki, amma bai kamata a dauki hakan da wasa ba.

Gwamnati tana bukatar goyon bayan ‘yan kasa domin cimma nasara.”

Sai dai kungiyar ta yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, bisa irin goyon bayan da suke baiwa hukumar.

Kungiyar ta kara da cewa gwamnatin ta nuna jajircewa wajen ganin an gudanar da aikin Hajji cikin gaskiya da adalci.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version