Daga Shafi’i Sani Muhammad
A wata ganawa da shugabannin hukumomin jin dadin Alhazai na Jihohi, Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya jaddada aniyarsa na gudanar da aikin Hajjin bana na 2025 cikin sauki da nasara. Ya bayar da wannan tabbacin ne a jawabinsa a taron da aka gudanar a hedikwatar hukumar NAHCON da ke Abuja.
Farfesa Saleh ya nuna godiya ga Allah Madaukakin Sarki da ya ba da damar gudanar da taron tare da jaddada sadaukarwar Hukumar na shawo kan kalubale da kuma sake mayar da hankali don samun inganta aiki.
A cikin jawabinsa, shugaban ya bayyana kalubale da dama da ya tarar lokacin da aka nada shi mukamin, da suka hada da ikrarin da ba a warware ba da kuma cikas wajen gudanar da ayyukan da suka kawo tasgaro ga ci gaban wasu muhimman ayyuka.
Ya kuma baiwa masu ruwa da tsaki tabbacin ci gaba da kokarin shawo kan wadannan matsalolin. “Alhamdulillah, a yau dukkanmu muna nan a matsayin abokan aiki, muna hada kawunanmu wuri guda domin magance kalubalen da ke gabanmu da kuma yin aiki a matsayin wata babbar kungiya domin tallafa wa daya daga cikin shika-shikan Musulunci,” inji shi.
Ya bayyana wasu daga cikin batutuwan da ake ta cece-kuce da su kawo yanzu, da suka hada da mayar da Riyal 150 na Saudiyya da rashin rashin da wutar lantarki ingantacciya a lokacin aikin Hajjin 2023.
Farfesa Saleh Usman ya tabbatar da cewa shugabancinsa na aiki tukuru don ganin an daidaita kudaden hidimar kashi 2% da aka warewa hukumar alhazai ta jiha dangane da aikin Hajjin 2024.
Shugaban ya kuma yi alkawarin biyan dukkanin wasu hakkoki da aka nema wadanda suka yi daidai da doka, tare da aza harsashin wani sabon babi na ayyukan NAHCON. Farfesa Saleh ya yi kira ga shugabannnin hukumomin alhazai na jahohi dasu gaggauta sanya kudade ga Hukumar domin samun damar yin shiri da wuri, da suka hada da samar da gidaje masu araha da dacewa a Madina, Makkah, Mina da Mashaer.
Ya kuma sanarwa da taron cewa zai fara ziyarce-ziyarce a shiyyoyin kasar nan guda shida domin tattaunawada malaman addini da sarakunan gargajiya domin samun goyon baya da albarkar aikin Hajjin 2025 da kuma ziyarar farko kafin aikin Hajji a kasar Saudiyya wanda zai gudana a watan Janairun 2025 wanda ya kunshi wakilai daga duka NAHCON da shugabannin hukumomin jin dadin Alhazai na Jihohi wadanda za su halarci tarukan shirye-shiryen aikin Hajji, tare da kammala yarjejeniya da hidimar alhazai, da kuma duba shirye-shirye a Jeddah.
Shugaban hukumar ta NAHCON ya kuma jaddada muhimmancin hada kai, inda ya bayyana ma’aikatan NAHCON da shuwagabanni/masu ruwa da tsaki na jahohi a matsayin manyan ginshikan hukumar.
Ya bukaci masu ruwa da tsaki da su hada kai a matsayin abokan aiki daya domin cimma manufa daya ta samar da aikin Hajji mai cike da inganci ga alhazan Najeriya.
A cikin kalamansa, “Na zo nan ne da kyakkyawar niyya da kuma tsare-tsare masu yawa na kawo sauyi fasalin Hukumar.
Mu bude sabon shafi mu sanya Hukumar Kula da Jin Dadin Alhazai ta Jiha ta NAHCON ta zama abin koyi don jin dadin Alhazan Najeriya,” inji shi.
Shi ma da yake nasa jawabin, Kwamishinan aiyuka na hukumar, Prince Anofi Olarewaju Elegushi ya bayar da bayanai kan kalandar Hajji ta 2025, inda ya bayyana cewa an raba takardar jagora mai shafuka 51 daga ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya don daidaita ayyukan.
An yi kira ga masu ruwa da tsaki da su fahimci ka’idojin da kuma bin ka’idojin aiki.
Taron ya kuma tabo batutuwan da ba a warware su ba daga aikin Hajjin 2024 inda Kwamishinan hukumar mai Kula da Ma’aikata da Kudi (PPMF), Aliu Abdulrazak ya bayyana cewa Shugaban Hukumar NAHCON ya ba da izinin fara biyan kudaden da Jihohi ke biya bayan an kammala sulhu da su da sashen Kudi da Asusu.
An kammala taron inda shugaban ya yi addu’ar Allah ya yi masa jagora da nasara, tare da jaddada kudurinsa na hada kai da duk masu ruwa da tsaki domin isar da sako mai inganci. Ya nanata muhimmancin hadin kai tare da yin kira ga masu ruwa da tsaki da su rungumi zaman lafiya domin samun nasarar aikin Hajji na shekarar 2025 tare.