Daga Shafii Sani Mohammed Da Abdul Abba Hukumar Alhazai ta Ƙasa ta Najeriya (NAHCON) ta karɓi wata babbar tawaga daga Masarautar Saudiyya, Ma’aikatar Hajji da Umrah, ƙarƙashin jagorancin Farfesa Dakta Ghassan Al-Nuaimi, a Hajj House da ke Abuja, a matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen farko na ayyukan Hajji da Umrah na 2026, tare da gabatar da wannan taro gabanin ziyarar aiki ta farko da Ministan Hajji da Umrah na Saudiyya zai kawo Najeriya.

KARANTA LABARI MAKAMANCIN WANNAN: Hajjin 2026: Muhimman Ka’idojin Lafiya da Dukkan Maniyyata Dole Su Bi – NAHCON

A jawabin buɗe taron, Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya yi maraba da tawagar Saudiyya zuwa Hajj House tare da bayyana farin cikinsa na karɓar bakuncinsu. Ya yi kira da a ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa da fahimtar juna tsakanin NAHCON da Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya, tare da gabatar da buƙatar ƙarin kujerun Hajji, inda ya bayyana cewa Najeriya ta riga ta cika adadin kujerun da aka ware mata.

A yayin taron, Kwamishinan Ayyuka na NAHCON, Yarima Anofiu Elegushi, ya yi wa tawagar bayani kan matakin shirin da Najeriya ta kai dangane da Hajjin 2026. Bayanin ya haɗa da shirye-shiryen farko, tattaunawa da kamfanonin jiragen sama, tsare-tsaren masauki a Makkah da Madinah, da kuma tsarin tura bayanan alhazai kafin isowarsu. Ya jaddada cewa ba za a bari wani alhaji ya bar Najeriya ba sai an kammala dukkan takardunsa kuma an tura su aƙalla awanni 72 kafin tafiya, bisa tsauraran ƙa’idojin Saudiyya.

Manyan ƙalubalen aiki da aka tattauna sun haɗa da raguwar kujerun Hajji, matsalolin masauki, ƙarancin damar jigilar jiragen sama, da jinkirin bizar Umrah da ke shafar masu shirya tafiye-tafiye. NAHCON ta nemi ƙarin kujerun Hajji tare da roƙon sa-hannun Saudiyya kan rabon masauki da amincewar jiragen sama, sannan ta gabatar da damuwa kan matsalolin biza da ke maimaituwa. Tawagar Saudiyya ta amince za ta duba waɗannan matsaloli ta hanyoyin fasaha da suka dace.

Tawagar Saudiyya ta jaddada muhimmancin bin jadawalin Hajji na ƙasa da ƙasa ba tare da kaucewa ba, tana mai bayyana cewa shirye-shirye na wuri-wuri wajibi ne kuma ba lallai a ba da ƙarin lokaci ba. Haka kuma an bayyana sabbin buƙatun lafiya da tsaro, ciki har da bin ƙa’idojin lafiya da aka sabunta ga alhazai.

NAHCON ta kuma bayyana matakan da take ɗauka don magance matsalar wuce lokacin zama (overstay), ciki har da shirin ɗaukar bayanan biometric da kuma amfani da tsarin bin diddigin alhazai na (centralized pilgrim tracking system).

A nasa jawabin, Shugaban Cibiyar Hajji ta Najeriya (Hajj Institute of Nigeria), Farfesa Maitulare, ya yi kira da Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya ta ba Cibiyar cikakkiyar sahalewa, tare da ba da shawarar a yi amfani da ita wajen horas da masu kula da Hajji da kuma yaɗa sabbin manufofi da ƙa’idojin Hajji da Umrah. NAHCON ta kuma gabatar da buƙatar horas da ma’aikatanta ta tsari daga masana’antar Hajji da Umrah ta Saudiyya domin ƙara ƙarfafa ƙwarewa wajen kula da alhazai.

Dukkan ɓangarorin sun jaddada ƙudurin ci gaba da haɗin gwiwa, inda tawagar Saudiyya ta yi alƙawarin ci gaba da bayar da goyon bayan fasaha da hulɗa ta hanyoyin diflomasiyya domin magance ƙalubalen aiki, tare da tabbatar da gudanar da Hajjin 2026 cikin tsaro, sauƙi da nasara ga alhazan Najeriya, bisa hangen nesa da jagorancin NAHCON ƙarƙashin Farfesa Abdullahi Saleh Usman.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version