Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta karfafa matakan sa ido a Madinah yayin da sama da mahajjata 17,000 daga Najeriya suka isa birnin domin gudanar da aikin Hajjin 2025.
Domin tabbatar da cewa mahajjata suna samun abinci mai kyau da lafiya, Kwamitin Ciyar da Mahajjata na Madinah karkashin jagorancin Alhaji Abdullahi Kabir na NAHCON yana ci gaba da sa ido kan harkokin abinci na yau da kullum. Kwamitin na tabbatar da bayar da karin kumallo da abincin dare ga kowanne mahajjaci.
A yayin wani duba da kwamitin ya gudanar, Alhaji Kabir ya jaddada cewa kulawar NAHCON ba wai kan abinci kawai take ba. “Mun kuduri aniyar tabbatar da mutuncin kowanne mahajjaci ta hanyar abincin da muke bayarwa. Ba abinci kawai muke bayarwa ba, muna kula da kimar ɗan Adam,” in ji shi.
Kamfanoni guda bakwai ne ke da alhakin ciyar da mahajjatan Najeriya a Madinah, wadanda suka hada da: Africana Home Restaurant, Amjad Alghraa, Al-Andalus, Mawasim Khairat, Na’a Azad, Zowar Muktara, da Kabala Catering. Kwamitin na duba kowane ɗayan wadannan dakunan girki akai-akai domin tantance tsafta, kayan aiki, ingancin sinadaran abinci da kuma kwarewar ma’aikata.
Wani muhimmin sharadi da NAHCON ta gindaya shi ne cewa sai an dauki ‘yan Najeriya a matsayin masu dafa abinci da kuma masu taimako, domin a tabbatar da cewa abincin ya dace da dabi’unmu, tare da samar da aikin yi ga ‘yan Najeriya a lokacin aikin Hajji.
Lokacin da suke gudanar da bincike, mambobin kwamitin na duba dukkan kayan abinci da za a yi amfani da su domin tabbatar da cewa sun cika ka’idojin gina jiki kuma ba su wuce lokacin amfani ba. Haka kuma NAHCON ta haramta amfani da sinadarai na ƙari (artificial additives) tare da tilasta amfani da sinadarai na halitta domin tabbatar da lafiyar abinci da kuma asalin girke-girken Najeriya.
A wani taro da masu bayar da abinci, Ko’odinetan Madinah, Alhaji Abdulkadir Oloyin, ya gargadi masu abinci game da amfani da kwantena marasa inganci. “Ba za mu amince da amfani da kwantena marasa karko ba. Abinci dole ne ya kasance cikin tsafta kuma a ba da shi cikin mutunci,” in ji shi.
Kwamitin ya kuma jaddada cewa dole ne a bi tsarin girke-girken abinci na Najeriya kamar yadda NAHCON ta amince da shi, domin tabbatar da cewa mahajjata suna jin kamar suna gida.
Yayin da hajjin ke kara kamari, tsarin kulawa da ciyarwa da NAHCON ke gudanarwa a Madinah na nuna yadda hukumar ke tsayawa tsayin daka wajen kula da jin dadin mahajjatan Najeriya.