Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta amince da sabon tsarin kayan tafiya ga alhazan Najeriya da za su sauke farali a Hajjin 2026, inda ta umurci dukkan kamfanonin jiragen sama da aka amince da su su ba wa kowane alhaji damar ɗaukar jakunkuna biyu na kaya masu nauyin kilo 23, tare da jakar hannu guda ɗaya mai nauyin kilo 8 a tafiyar dawowa daga Saudiyya.

Hajj Chronicles ta gano cewa wannan umarni yana kunshe ne a cikin takardun da aka bai wa kamfanonin jiragen sama da za su yi aikin jigilar alhazan Hajjin 2026.

Binciken majiyar Hajj Chronicles ya nuna cewa an fitar da umarnin ne a cikin wata wasiƙa mai kwanan wata 23 ga Disamba, 2025, wadda Kwamishinan Ayyuka na NAHCON, Anofiu Olarenwaju Elegushi, ya sanya wa hannu, inda aka fayyace sharudda da ka’idojin aikin da kamfanonin jiragen za su bi.

An Kawar da Tsarin Jaka Guda mai Nauyin kilo 32kg

Sabon tsarin ya kawo ƙarshen tsohon tsarin da ke bai wa alhaji damar ɗaukar jaka guda ɗaya mai nauyin kilo 32, tare da jakar hannu kilo 8 kacal.

A ƙarƙashin sabbin ƙa’idojin Hajjin 2026, kowane alhaji zai riƙa ɗaukar jakunkuna biyu na kilo 23 kowanne, wanda ke nufin jimillar kilo 46 na kaya, ba tare da haɗa jakar hannu ba.

Daidaituwa da Tsarin Kasa da Kasa

Ta hanyar wannan sabon tsari, NAHCON ta daidaita alhazan Najeriya da tsarin jigilar kaya na jiragen sama da ake amfani da shi a ƙasashe da dama a duniya.

Wannan mataki ya kuma magance koke-koken da alhazan Najeriya ke yi tun da dadewa kan tsauraran ƙa’idojin kaya da rashin daidaito, musamman idan aka kwatanta da alhazan wasu ƙasashe da ke amfani da jirage iri ɗaya. Alhazan da ke tafiya ta hannun Hukumar Jin Daɗin Alhazai na Jihohi yanzu za su samu damar kaya iri ɗaya da masu zaman kansu da kuma na ƙasashen waje.

Rage Wahala da Kuɗin Karin Kaya

Ana sa ran sabon umarnin zai rage wahalar da alhazai ke fuskanta wajen ɗaukar kayansu, ya sauƙaƙa ɗaukar kayan kyauta da na amfanin kai, tare da rage matsalolin biyan kuɗin karin Kaya a filayen jiragen sama.

Majiyar Hajj Chronicles ta fahimci cewa NAHCON za ta sa ido sosai kan bin wannan umarni daga kamfanonin jiragen sama domin tabbatar da cikakken aiwatar da shi a Hajjin 2026.

Wannan labari na ci gaba da gudana. Hajj Chronicles za ta ci gaba da kawo muku sahihan labarai da sabbin bayanai kan yadda za a aiwatar da wannan tsari.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version