Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta sanar da Ƙananan sauye-sauye a ma’aikatanta bisa ga shawarar da Kwamitin Hukumar ya cimma a zama na 14 da aka gudanar daga ranar 26 zuwa 27 ga watan Agusta, 2025.

A sanarwar da Mataimakiyar Daraktar yada labarai da Dab’i ta hukumar, Fatima Sanda Usara ta sanayawa hannu, tace a  cikin sauye-sauyen, ɓangaren gudanarwa na Hukumar ya umarci ma’aikatan da aka ɗebo daga wasu ma’aikatu su koma inda aka ɗebo su wato Ma’aikatu, Hukumomi da Sassa (MDAs) nan take.

Waɗannan ma’aikatan sun karɓi takardun tura su ranar Alhamis, 4 ga Satumba, 2025.

Kwamitin ya bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne domin kawar da sake-sake, inganta aiki, da kuma sake tsarawa domin samun ingantaccen tsarin gudanarwa.

Hakan kuma zai ƙara ƙarfafa ma’aikata wajen yin aiki da ƙwazo.

Domin ƙara goyon bayan shirin gyare-gyare, Kwamitin ya amince da haɓaka hazakar wasu ma’aikata da suka cancanta tare da shirya horo ga dukkan ma’aikata.

An tsara wannan horo ne domin bai wa jami’an Hukumar ƙwarewa da basirar da ake buƙata wajen cimma manufofin NAHCON.

Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya tabbatar da cewa yan Hukumar gudnarwar na 5 zasu ci gaba da yin duk abin da ya dace wajen gina ƙwararrun ma’aikata masu ƙoƙari wajen cika nauyin da doka ta ɗora wa Hukumar domin kula da alhazai na Najeriya.

Haka kuma, Hukumar za ta ci gaba da gabatar da wasu gyare-gyare domin ƙara haɓaka aiki da ingantacciyar gudummawa.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version