Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) na sanar da al’umma, musamman maniyyatan Hajjin 2025, iyalansu da kuma masu ruwa da tsaki cewa, aikin jigilar maniyyata dawowa gida daga kasar Saudiyya ya samu gagarumin ci gaba sakamakon karuwar izinin tashin jirage da kamfanonin sufurin sama suka samu.
A cikin wata sanarwa da Fatima Sanda Usara, Mataimakiyar Daraktar yada Labarai da Dab’i ta hukumar, ta fitar, ta bayyana cewa tun daga ranar 22 ga Yuni, an raba har zuwa jirage guda bakwai a kullum ga kamfanonin jiragen saman Najeriya, da rabo kamar haka: 2-2-2-1. Sai dai ana fuskantar jinkiri sakamakon cunkoson sararin samaniya bayan kammala Hajji da kuma soke jirage saboda wasu dalilai.
Duk da wannan karin da aka samu na izinin tashin jirage, aikin dawo da maniyyata ba zai kammala a ranar 28 ga Yuni kamar yadda aka yi tsammani ba. Hukumar ta ce akwai yiyuwar aikin ba zai kammala ba sai a ranar Talata, 2 ga Yuli, 2025 – wato cikin kwanaki shida masu zuwa, matuƙar ba a sake fuskantar wani cikas ba.
Daga cikin maniyyata 41,668 da aka kai Saudiyya don gudanar da Hajjin bana, fiye da 27,316 sun riga sun dawo gida Najeriya. Wannan adadin bai haɗa da dubban maniyyatan da suka dawo ta jiragen kasuwanci ba saboda wasu buƙatu na gaggawa da suka taso musu a gida.
Daga cikin adadin da suka rage:
Max Air na da maniyyata 6,019 da zai iya jigila a kullum har 1,120, ta hanyar jirage biyu masu kujera 560 kowanne.
UMZA Aviation Services na da saura 4,850, da zai jigila da jirage biyu masu kujeru 484 da 312, wanda ya kai jimillar kujeru 796.
FlyNas ya rage da maniyyata 2,480 kuma yana da ƙarfin ɗaukar 819 a rana.
Air Peace na da saura 1,635 da jirginta mai kujeru 315.
NAHCON ta tabbatar da jajircewarta wajen ganin an dawo da dukkan maniyyata cikin lokaci