Daga Shafii Sani Mohammed, Babban Jami’in Yada Labarai na NAHCON. Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta kara kaimi wajen shirye-shiryen gudanar da Hajj na shekarar 2026, tare da mayar da hankali kan daidaiton aiki, hadin kai tsakanin sassa, da inganta ayyuka ga alhazai. Wannan kudiri ya kara karfi ne a wani taron tantance ayyuka da aka gudanar a Hajj House, wanda ya samu halartar Shugaban Hukumar, Kwamishinoni, Daraktoci da wakilan Acosta Media.
Karanta Wani Labarin Makamancin Wannan : Shugaban NAHCON Ya Kaddamar da Tawagar Nusuk Masar ta Hajjin 2026
A matsayin wani bangare na horon ma’aikatan NAHCON na duk wata, taken na yau ya mayar da hankali ne kan Ayyukan Madina. Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya bude zaman da jaddada bukatar kwarewa, gaskiya da hadin kai tsakanin dukkan sassan aiki. Ya ce Saudiyya na canza dokoki da tsarin fasaha akai-akai, lamarin da ya sanya wajibi ma’aikatan NAHCON su kasance masu sabunta ilimi da bin zamani.
“Dokoki da fasahohin Saudiyya na sauyawa kowace shekara, kuma bukatun alhazai daga Najeriya suna karuwa. Don haka dole mu kasance masu cikakken shiri, sabuwar masaniya da ingantaccen daidaiton aiki,” in ji Shugaban.
Yayin da yake tabo kalubalen shekarar da ta gabata, Farfesa Usman ya tunatar da ma’aikata cewa darussan da aka koya su zama hanya ta inganta aikin bana.
“Mun gani a inda muka samu matsaloli. Bana dole mu kara ladabi, hadin kai da jajircewa don baiwa alhazai mafi kyawun hidima,” kamar yadda yace.
Ya kuma yi bayani kan muhimmancin fahimtar gibin da aka fuskanta a bara. Shugaban ya karfafa ma’aikata kan su rika tambaya, musayar ilimi, da taimakon juna, yana mai jaddada cewa ayyukan Hajj na sauyawa kowace shekara ko da ga jami’an da ke zaune a Saudiyya.
A nasa jawabin, Kwamishinan Sashen Tsare-tsare, Bincike, Kididdiga, Bayani da dakin karatu (PRSILS), Farfesa Abubakar Yagawal, ya yi kira mai karfi da a tabbatar babu wani korafi daga alhazai a Birnin Manzon Allah, Madina.
Ya jaddada nauyin da duk wani korafi a Madina yake dauke da shi:
“Don Allah ku kokarta ku warware musu matsaloli, domin duk wani korafi a Madina, a ganina, korafi ne ga Manzon Allah ﷺ. Don haka, kada ku bari alhazanmu su samu wata matsala ko na abinci, ko masauki, ko wajen ziyara.”
Farfesa Yagawal ya bukaci jami’ai su jagoranci alhazai tun daga tashar jirgin sama ta Madina, zuwa rabon masauki da dukkan ayyukan da suka shafesu.
“Idan alhaji ya samu nutsuwa a Madina, tafiyarsa za ta kasance da annashuwa gaba daya. Amma idan ya fara da matsala a Madina, sakamakon na iya yin muni,” Inji Yagawal.
Ya yaba da jajircewar jami’an NAHCON da ke aiki tukuru a filin jirgin Madina, sannan ya bukaci karin himma:
“Na ga yadda tawagarmu ke aiki ba dare ba rana a Madina. Amma don Allah, ku ninka kokarinku wajen faranta ran alhazai.”
Tun da farko a cikin taron, Daraktan Ma’aikata da Albarkatun Dan Adam, Alhaji Alidu Shutti, ya yi maraba da mahalarta taron kuma ya tabbatar da kudirin Hukumar na karfafa gwiwar ma’aikata kafin Hajj 2026.
Ya shawarci ma’aikata da su shiga sosai cikin taron, yana mai bayyana cewa wasu daga cikin gabatarwar da ake yi a irin wadannan taruka za su zama tambayoyi a jarabawar karin girma da Hukumar za ta gudanar.
Zaman ya sake tabbatar da kudirin NAHCON na inganta ayyuka, daidaiton aiki da samar da kyakkyawar tafiyar Hajj ga alhazai daga Najeriya. Tare da Shugabanci na jaddada tsari, hadin kai da ingantacciyar hidima musamman a Madina, inda yawanci tafiyar Hajj ke farawa NAHCON na fatan zarce dukkan matakai da na shekarun baya yayin da ake shirin gudanar da Hajj 2026 mai nasara.
