Da yake zantawa da Freedom Radio Kaduna, Shugaban Hukumar Farfesa Abdullahi Saleh Usman Pakistan, ya ce tallan daukar aikin wata zamba ce da wasu marasa kishin kasa suka tsara domin damfarar masu son yin aiki a Hukumar.
Ya ce a halin yanzu, babban abin da ya fi damun Hukumar shi ne gudanar da aikin Hajji ba tare da matsala ba.
Shugaban ya gargadi masu hannu cikin wannan lamari da su daina yaudarar, ko kuma su fuskanci fushin doka.
Farfesa Abdullahi Saleh ya bayyana cewa ana kokarin ta hanyar jami’an tsaro da abin ya shafa domin bankadowa tare da bin diddigin wadanda suke da hannu wajen tallata ayyukan yi na bogi da aka baiwa Hukumar.
Ya shawarci al’umma da su rika neman karin haske kan duk wani bayani da ake yadawa a kafafen sada zumunta na zamani, domin hukumar tana bin dokoki da ka’idojin daukar ma’aikata, yana mai cewa a lokacin da ya dace kuma hukumar za ta sanar da jama’a yadda ya kamata ta hanyoyin da aka amince da su a hukumance.