Hukumar alhazai ta kasa NAHCON tana sanar da al’umma cewa ta rabada kudaden da suka kai naira biliyan 4,479,362,880.00 (Biliyan hudu, da dari hudu da saba’in da tara, dubu dari uku da sittin da biyu, da naira dari takwas tamanin) ga hukumomin Jin Alhazai na Jihohi, Babban Birnin Tarayya (FCT) da kuma banagaren Sojoji.

A sanarwar da shugaban sashen hulda harkokin hulda da jama’a na hukumar, Muhammad Ahmed Musa ya sanyawa hannu, t ace wadannan kudaden sun shafi ayyukan samar da wutar lantarki na Masha’ir da hukumomin Saudiyya ba su yi yadda ya kamata ba a lokacin aikin Hajjin 2023.

Kazalika, Hukumar ta mayar da kudi N917,148,479.99 (miliyan dari tara da goma sha bakwai, dubu dari da arba’in da takwas, da dari hudu da saba’in da tara, kobo casa’in da tara) ga Kamfanonin jirgin yawo guda 192 da suka shiga aikin Hajjin 2023.

Wannan adadin kudade an fitar dasu ne domin rabawa ga alhazansu, yayin da sauran kamfanonin su ma za a mayar musu da nasu kudaden bayan an yi sulhu.

Wannan mayar da kudade ya nuna jajircewar NAHCON, a ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, domin tabbatar da gaskiya da rikon amana a harkokin tafiyar da ayyukan Hajji.

Ana shawartar dukkan Alhazan da suka halarci aikin Hajjin 2023 da su tuntubi Hukumomin Jin Dadin Alhazai na Jihohinsu, ko kuma kamfanonin jiragen yawo domin neman a mayar musu da kudadensu.

Kowanne Mahajjaci, yana da hakkin karbar kudi N61,080.00.

(Dubu Sittin da Daya, Naira Tamanin kacal). An kuma sanya cikakken bayanin adadin alhazai na kowacce jaha na kudin da zasu karba cikin wannan sanarwa.

A saboda haka sai hukumar ta NAHCON ta yi kira ga dukkanin wanda ked a niyyar zuwa aikin Hajin 2025 da ya biya kudinsa ga hukumar Alhazai ta jaharsa

Wannan matakin yana da matukar muhimmanci don tabbatar da isar da kudade ga hukumar NAHCON a kan lokaci, ta yadda za a samu saukin shirye-shiryen aikin Hajjin 2025 da wuri bisa ka’idojin da masarautar Saudiyya ta gindaya.

Domin tabbatar da gaskiya da kididdiga, NAHCON ta yi kira ga Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC), da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) da sauran hukumomin tsaro da abin ya shafa da su sanya ido sosai kan yadda za a dawo da kudaden.

Wannan haɗin gwiwar yana nufin tabbatar da cewa an biya duk kudaden da aka mayar da su daidai kuma an kai ga waɗanda suka amfana ba tare da wani bambanci ba.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version