Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazan Jihar Sokoto (PWA), Alhaji Aliyu Musa, ya duba aikin sarrafawa da loda fasfofin maniyyata a manhajar E-Track da ke gudana a halin yanzu.
A sanarwar da Shugaban sashen yada labarai da sadarwa na Hukumar Faruku Umar ya sanyawa hannu, yace ziyarar dubawa ta gudana ne a ofisoshin wucin-gadi na Hukumar da ke cikin Sansanin Alhazan NAHCON da ke Modorawa.
Shugaban ya samu rakiyar mambobin shugabancin Hukumar tare da wasu mambobin Kwamitin Gudanarwa.
A yayin ziyarar, Alhaji Aliyu Musa ya duba Cibiyar Fasahar Sadarwa da Bayanai (ICT) ta Hukumar, inda ake gudanar da aikin loda fasfofin maniyyata a manhajar E-Track.
Haka kuma ya duba wasu muhimman ofisoshi da suka haɗa da Ofishin Gudanarwa, Ofishin Da’awah da Irshad, Ma’ajiya, da Ofishin Ma’aikata Gaba ɗaya.
Manufar ziyarar ita ce tantance matakin shiri da kuma tabbatar da cewa dukkan hanyoyin aiki suna gudana cikin tsari da inganci, daidai da ka’idojin gudanar da aikin Hajji
