Shugaban Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) kuma Babban Jami’in Gudanarwa, Farfesa Sheikh Abdullahi Saleh Usman, ya yi murabus daga mukaminsa, inda ya bayyana dalilan hakan a matsayin na kashin kai.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Farfesa Usman ya ce murabus ɗin ya fara aiki ne daga ranar Litinin, 9 ga watan Fabrairu, 2026, bayan abin da ya bayyana a matsayin zurfin tunani, addu’a, da shawara da iyalansa.

Ya bayyana cewa ya miƙa takardar murabus ɗinsa a hukumance ga Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, bisa tanadin Sashe na 3(6) na Dokar Kafa Hukumar NAHCON ta shekarar 2006.

Farfesa Usman ya nuna godiyarsa ga Shugaba Tinubu bisa damar da aka ba shi ta yi wa ƙasa da al’ummar Musulmi hidima, yana mai cewa wannan naɗi babban abin alfahari ne a gare shi.

Haka kuma ya gode wa Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, bisa jagoranci, ƙarfafawa, da goyon bayan da ya ba shi a lokacin da yake kan muƙaminsa.

Tsohon Shugaban NAHCON ɗin ya kuma gode wa mambobin kwamitin gudanarwa, shugabanni, da ma’aikatan hukumar bisa haɗin kai da jajircewarsu wajen aiki.

Ya kuma yaba da gudunmawar Hukumomin Jin Daɗin Alhazai na Jihohi, kamfanonin yawon Hajji, kamfanonin jiragen sama da sauran masu ba da hidima, da kuma abokan hulɗa a Ƙasar Saudiyya, bisa rawar da suka taka wajen inganta ayyukan Hajjin Najeriya.

Farfesa Usman ya jaddada cewa murabus ɗinsa ya samo asali ne kawai daga dalilai na kashin kai, ba wai saboda wata rashin jituwa da hukumar, gwamnati, ko manufofinta ba.

A ƙarshe, ya yi addu’ar fatan alheri ga NAHCON, shugabannin ƙasa, da dukkan alhazai na gaba, yana roƙon Allah Ya karɓi ayyukan da aka yi, Ya kuma ba mahajjata Hajji nagari.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version