Shugaban Hukumar JAlhazai ta Najeriya (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya bayyana godiya ta musamman ga Allah Madaukakin Sarki bisa nasarar gudanar da aikin Hajjin 2025, yana mai cewa nasarar ta samo asali ne daga albarkar Allah da hadin kan dukkan masu ruwa da tsaki.

KARANTA LABARI MAKAMANCIN WANNAN: Gwamnatin Tarayya Ta Yabawa Shugaban NAHCON Bisa Kokarin Inganta Jin Dadin Alhazai- Daga Nura Ahmad Dakata

Farfesa Saleh ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano, jim kadan bayan dawowarsa daga kasa mai tsarki inda aka kammala aikin Hajjin bana.

 

A cewarsa, nasarar da aka samu ba tasa kadai bace, ko ta hukumar NAHCON, sai dai wata baiwa ce daga Allah wanda Ya sa aikin ya tafi lafiya kuma cikin nasara.

 

“Nasararmu a wannan shekarar ta Hajji ta samu ne da yardar Allah. Ba tawa bace, ba kuma ta hukumar NAHCON kadai ba Allah ne Ya albarkaci wannan aiki, Ya shiryar da mu duka cikin hanya madaidaiciya,” in ji shi.

 

Ya yaba da hadin kai da halin kirki da alhazan Najeriya suka nuna, tare da jinjinawa gudunmuwar da sauran bangarori suka bayar, ciki har da kwamitocin Majalisar Dattawa da ta Wakilai masu kula da harkokin Hajji.

 

“Kun ji komai daga bakin shugabanninmu daga kwamitocin Majalisa. Sun wakilce ni kuma sun bayyana abinda ke cikin zuciyata. Ina kuma matukar godiya ga kafafen yada labarai bisa kokarinku na isar da sakonmu ga jama’a. Muna godiya da hadin kai da sadaukarwarku,” ya kara da cewa.

 

Shugaban NAHCON ya jinjina wa goyon bayan da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima suka baiwa hukumar, yana mai cewa irin wannan goyon baya ne ya taimaka wajen nasarar gudanar da aikin Hajjin bana.

 

“Muna godiya matuka ga Gwamnatin Tarayya. Shugaba Tinubu ya bamu cikakken goyon baya. Mataimakin Shugaba Shettima wanda mukewa aiki a ofishinsa, yana bin diddigin abubuwan da muke yi yana tambaya yau me ke faruwa, gobe me za ku yi. Wannan kulawa tasa muka yi aiki kamar iyali daya, muna da hadin kai da girmama juna,” in ji shi.

 

Yayin da ake shirin Hajjin shekarar 2026, Farfesa Saleh ya tabbatar da cewa NAHCON ta koyi darussa da dama daga aikin bana, kuma tana shirye fiye da da.

 

“InshaAllah, da irin kwarewar da muka samu da darussan da muka koya a bana, mun shirya sosai don gudanar da aikin Hajjin shekara mai zuwa. Muna rokon Allah Madaukakin Sarki Ya sanya Hajjin 2026 ya fi na bana nasara da albarka,” ya kammala.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version