Shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman da tawagarsa, , sun ziyarci Shehun Borno, Alhaji Abubakar ibn Umar Garbai El-Kanemi.

IMG 20241212 WA0050

A jawabinsa yayin ziyarar, Farfesa Saleh Usmanya ya ce tawagar ta kasance a fadar Shehu ne domin neman goyon bayansa da kuma shawarwarin inganta harkokin aikin Hajji.

 

Ya kuma bayyana irin shirye-shiryen da aka yi ya zuwa yanzu na aikin Hajjin 2025.

IMG 20241212 WA0051

Da yake mayar da jawabi, Shehun Borno ya yi kira ga Hukumar NAHCON da ta kara himma wajen inganta aikin Hajji, ya yi tsokaci game da kaya da motocin bas na jigilar alhazai a Saudiyya.

IMG 20241212 WA0049

Shugaban Hukumar NAHCON a ranar Larabar da ta gabata, yayin wata ganawa da shugabannin hukumomin jin dadin Alhazai na Jiha, ya ce zai fara rangadin shiyyoyin siyasa guda shida na kasar nan domin ganawa da malaman addini da sarakunan gargajiya domin samun goyon baya da albarka domin samun nasarar. 2025 Hajj.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version