Daga Suwaiba Ahmed
Tawagar ma’aikata 36 da jami’an lafiya daga Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta isa Masarautar Saudiyya domin fara shirye-shiryen gudanar da aikin Hajji na bana. Tawagar ta sauka a Filin Jirgin Sama na Sarki AbdulAziz da ke Madinah da safiyar Talata, 6 ga Mayu, 2025.
Jagoran tawagar, Alhaji Alidu Shuti wanda shi ne Mataimakin Kwamishinan ayyuka a Makkah, ya jagoranci wakilai daga kwamitoci daban-daban da suka hada da Masauki, Abinci, Lafiya, Taron Karbar Bakuncin Kasa, Sarrafa Fasfo, E-Track, Hijira, Tafwij da kuma Sashen Yada Labarai.
Ayyukan wadannan kwamitoci shi ne tabbatar da cika dukkanin shirye-shirye kafin isowar jirgin farko na alhazai daga Najeriya, wanda aka shirya zai tashi ranar 9 ga Mayu, 2025.
A ranar Litinin kafin tafiyar, Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya bukaci tawagar da su yi aiki tukuru wajen aiwatar da aikin da aka dora musu, yana mai cewa nasarar aikin Hajjin bana na da alaka da yadda tawagar za ta gudanar da ayyukanta a matakin farko.
Isowar wannan tawaga na nuna fara shirye-shiryen aikin Hajji na 2025 a kasa mai tsarki.