Wani tsohon Alhaji mai suna Muhammad Suleman Gama, ya kare Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman, kan abin da ya bayyana a matsayin “tuhume-tuhumen banza” daga wasu mutane masu neman biyan buƙatun kansu.

Gama, wanda ya ce ya yi aikin Hajji fiye da sau 20, ciki har da na bana, ya bayyana cewa Hajjin 2025 ƙarƙashin shugabancin NAHCON ya samu gagarumar nasara musamman wajen kula da walwalar alhazai da ingancin ayyuka.

A cewarsa, an tsara batun masauki, abinci, sufuri da kuma hulɗar diflomasiyya da hukumomin Saudiyya yadda ya dace, lamarin da ya sa wannan hajji ya zama ɗaya daga cikin mafi nasara a ‘yan shekarun nan.

“Abin takaici ne yadda wasu mutane marasa kirki ke ƙoƙarin bata sunan Shugaban NAHCON kawai don sun kasa samun mukamai ko kuma ba a amince da buƙatunsu na kai-tsaye ba,” in ji shi.

Ya zargi ɗaya daga cikin masu suka da cewa shi ne ya taɓa yin lallami na neman aiki a NAHCON amma bai samu ba, daga bisani ya fara wallafa sharhi marasa inganci ba tare da ya halarci aikin Hajji ba.

“Idan dai wani daga cikin alhazan da suka halarci aikin Hajji na bana ne ya yi suka, za mu fahimta. Amma wani da bai shiga aikin ba ya yi ƙarya yana bata suna, hakan ba adalci ba ne,” inji Gama

Dangane da ikirarin cewa Farfesa Sale ya yi watsi da gudunmawar wasu ƙungiyoyin addini, Gama ya ce wannan “ƙarya ce”, yana mai bayyana cewa a karon farko, NAHCON ta haɗa malamai daga kowane bangare don tallafa wa alhazai a Makka, Madina da Mina.

Haka kuma, ya yi kira ga masu suka da su bari Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) da sauran hukumomi su kammala bincikensu kafin yanke hukunci, yana gargadi kan hare-haren son zuciya da ka iya lalata martabar hukumar.

“Farfesa Abdullahi yana fuskantar suka marasa tushe ne kawai saboda wasu ba sa son shi a wannan kujera. Ya kamata su bar shi ya nuna kwarewarsa kafin su yanke hukunci,” in ji shi.

Wannan gogaggen Alhaji ya bukaci masu ruwa da tsaki da su gane nasarorin da aka samu a aikin Hajjin 2025, yana mai jaddada cewa duk wani jagora da ya ke da muhimmiyar alhakin ƙasa dole ya fuskanci yabo da suka.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version