A cikin wata hira da wata Jarida, Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya mayar da martani kan zarge-zargen karkatar da kuɗaɗe da ake yi wa hukumar da kuma binciken da Hukumar EFCC ke gudanarwa. Haka kuma ya bayyana sabbin matakan da ya ɗauka wajen kare walwalar maniyyata da kuma rage musu kuɗin aikin Hajji.

KARANTA LABARI MAKAMANCIN WANNAN : Mun Gano Wani Shiri na Bata Sunan Shugaban NAHCON – Kungiya

Tambaya: Waɗanne sabbin abubuwa ka kawo tun bayan hawanka kujerar shugabancin NAHCON?

Amsa: Da na hau, na fara nazarin manufar hukumar, wacce ginshikinta shi ne kula da walwalar maniyyata. Mun tuntuɓi masu ba da hidima don samun rangwame a kuɗaɗen da ake cajar maniyyata. Alhamdulillah, mun samu nasara. Idan ba don haka ba, aikin Hajjin bara zai iya kai wa sama da Naira miliyan 11. Mun rage kuɗin sabis a Mina, Arafat da Muzdalifa da Riyal 720 a kan kowane maniyyaci. Haka kuma mun samu ragin Riyal 200 a Madina da kuma Riyal 303 a sufuri daga Makka zuwa Mina.

Mun kuma tilasta wa jiragen da ke ɗaukar maniyyata karɓar kuɗi da naira, maimakon dalar Amurka. Wannan ya ceci maniyyata daga tasirin tashin farashin dala.

Mun roƙi Babban Bankin Ƙasa ya soke tsarin amfani da kati kawai wajen cire kuɗi a Saudiyya saboda yawancin maniyyata ba sa iya amfani da ATM, musamman a waje. Yanzu ana ba da kuɗi hannu kamar yadda aka saba.

Mun faɗaɗa tsarin asusun ajiya daga banki guda zuwa bankuna huɗu, domin a ba da dama ga dukkan sassan ƙasa. Haka kuma gwamnatin tarayya ta tallafa da kayan magunguna na daruruwan miliyoyi don rage nauyin da ke kan maniyyata.

Tambaya: EFCC ta gayyaci wasu ma’aikatan hukumar. Me zaka ce game da hakan?

Amsa: Hukumar gwamnati ce NAHCON, kuma hukumar bincike na da hurumin gudanar da bincike duk inda aka samu koke. Bayan aikin Hajjin bara, kowa ya yaba cewa shi ne mafi nasara tun kafuwar hukumar. Ban ji wata korafi daga maniyyata ba. Sai dai abubuwa suka sauya bayan dawowa. Na ji cewa yawancin korafe-korafen daga cikin ma’aikatan hukumar ne suka fito, saboda hassada ko rashin jin daɗi. Amma har yau babu wanda ya kawo ƙorafi a hukumance cikin gida.

Tambaya: Shin kana da buɗaɗɗen ƙofa don karɓar waɗannan ƙorafe-korafe?

Amsa: Eh. Ni malamin addini ne, wanda ya shafe shekaru ina wa’azi da jagoranci. Ba zan rufe ƙofa ga kowa ba. Na kuma kula da walwalar ma’aikata fiye da yadda aka saba, na biya bashin alawus da na tarar ya jima, kuma na ba su damar yin Hajji yayin aiki. Saboda haka ban yi tsammanin zarge-zargen nan ba.

Tambaya: Ana zargin ka da sauya dukkan masu yi wa alhazai hidima a Saudiyya?

Amsa: Wannan al’amari yana hannun masu bincike. Idan aka gayyace ni, zan bayyana. Ba zan yi tsokaci a yanzu ba saboda bincike yana gudana.

Tambaya: Ana kuma cewa kana da rauni a fahimtar Turanci, kuma wasu ’yan uwa na amfani da hakan don yaudare ka.

Amsa: Na yi karatu a Jami’ar Madina da Pakistan, sannan na yi digirin digirgir a Usmanu Danfodiyo. Yawancin karatuna da mu’amalata a aikin Hajji na da alaƙa da Larabci, wanda shi ne harshen Saudiyya. Na iya Turanci matuƙar da ba zan kasa fahimtar takardu ba. Game da ’yan uwa, na kawo ɗan uwana wanda ya yi aiki a gwamnati na tsawon shekaru 31, saboda ƙwarewarsa a gudanarwa. Sauran wanda ake cewa ni da shi dangi ne ba gaskiya ba. Na ɗauke shi ne saboda kwarewarsa a kuɗi.

Tambaya: Ana zargin cewa akwai nuna bambanci wajen rarraba tantuna?

Amsa: Tun farko akwai rabe-raben tantuna: na talakawa, Tent A da A+. Farashin ya bambanta, kuma duk mai biyan ƙarin kudi yana samun sabis na musamman. Wannan ba sabon abu ba ne.

Tambaya: Kana ganin waɗannan zarge-zargen cin hanci suna ɓata sunan hukumar?

Amsa: Eh, amma abin mamaki shi ne wannan hukumar ce kawai babbar hukuma a tarayya da dukkan ma’aikata musulmai ne. Duk da haka ana ta zarge-zarge. Ina ganin wannan daga hassada da son zuciya ya samo asali. Misali, gwamnatin tarayya ta bayar da tallafin Naira biliyan 90 don rage wa maniyyata nauyi a bara. Duk maniyyacin da ya bi ka’ida ya amfana. Don haka ina mamakin daga ina ake samo waɗannan zarge-zargen.

Tambaya: Shin kana jin tsoron binciken EFCC?

Amsa: Wallahi, babu tsoro. Na yarda cewa adalci zai bayyana gaskiya. Ban aikata abin da ake zargina da shi ba.

Tambaya: Yaya dangantakarka da sauran kwamishinoni a NAHCON?

Amsa: Na tarar da su a nan. Wataƙila wasu ba su ji daɗi ba saboda ni aka zaɓa. Amma na saba aiki da manyan ƙungiyoyi a Pakistan da kasashen Larabawa. Na yi ƙoƙarin yin adalci ga kowa, kuma hakan ya taimaka.

Tambaya: Pilgrims suna yawan kuka kan nisan gidaje daga Harami. Me kuka yi kan haka?

Amsa: A Madina, dukkan maniyyatan bana sun samu masauki mafi kusa da Masallacin Annabi fiye da kowanne lokaci. A Makkah kuwa, jihohi ne ke ɗaukar nauyin masaukin maniyyatansu, mu dai NAHCON muna duba inganci kafin amincewa. Amma tsarin gine-ginen sabuwar Makkah yana rage gidaje kusa da Harami, don haka hakan yana kawo ƙalubale.

Tambaya: Mene ne shawararka ga masu niyyar Hajji game da biyan kuɗi?

Amsa: Na riga na fara ganawa da malamai da hukumomi don a karfafa jama’a su biya da wuri. Wannan zai hana rikice-rikicen kudi daga Saudiyya. A bana mun fara karɓar ajiya na N8.5m. Ina sa ran kudin Hajjin bana zai ragu idan aka kwatanta da bara.

Tambaya: Ta yaya kuke rage kuɗin Hajji?

Amsa: Mun yi amfani da kusanci tsakanin wasu yankuna da Saudiyya wajen rage kudin jirgi. Yankin Arewa maso Yamma da Arewa maso Tsakiya sun samu ragin dala $116; Arewa maso Gabas $149; Kudu $138. Jimillar ragin ya kai Naira biliyan 50 da fiye.

Tambaya: Za ka kira wannan nasara taka?

Amsa: Ba zan kira ta tawa ba. Misali, a 2023 maniyyata sun biya kuɗin AC a Mina da Arafat amma ba su samu ba. Na mayar musu Naira biliyan 5.3, inda kowane maniyyaci ya karɓi N60,000 da ƙari. Hakan ne ma ya tabbatar da cewa mu muna tsoron Allah. Na kuma gayyaci EFCC da ICPC su kasance shaida wajen rabon kuɗin.

Tambaya: Shin ka taɓa jarabtuwa da amfani da waɗannan kuɗaɗe?

Amsa: A’a. Na san illar kuɗin haram. Na shafe shekaru 36 ina jagorantar masallacin Juma’a da yin wa’azi kan guje wa kuɗin haram. Abin da ya kamata ya ba mutane mamaki shi ne yadda na dawo da kuɗin, ba yadda aka batar da su ba.

(Daily Trust)

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version