Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) ta bayyana cewa Masarautar Saudiyya ta amince da ƙarin guraben Hajji 10,000 ga Najeriya domin aikin Hajjin shekarar 2027, sakamakon ci gaba da manyan tattaunawar diflomasiyya tsakanin Gwamnatin Tarayyar Najeriya da Masarautar Saudiyya.
A sanarwar da Shugaban sashen yada labarai da dab’i na Hukumar, Shafii Sani Mohammed ya fitar, wannan ƙarin gurabe ya sa jimillar adadin guraben Hajjin da aka ware wa Najeriya a shekarar 2027 ya tashi daga 50,000 zuwa 60,000.
Don fayyace yadda aka raba ƙarin guraben 10,000, an ware su kamar haka:
Gurabe 7,500 ga Hukumomin Jin Daɗin Alhazai na Jihohi, da hukumomi da kwamitocin da ke kula da aikin Hajji; sannan
Gurabe 2,500 ga kamfanonin shirya Hajji masu zaman kansu guda bakwai (7) da ke kan gaba.
Saboda haka, ƙarin guraben 10,000 na nufin faɗaɗa guraben da Najeriya ke da su a baya na 50,000, inda jimillar guraben Hajjin Najeriya na shekarar 2027 yanzu suka kai 60,000.
Shugaban Hukumar NAHCON, Ambasada Ismail Abba Yusuf, ya bayyana matuƙar godiyarsa ga Gwamnatin Tarayyar Najeriya, ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, bisa ci gaba da goyon baya, jagoranci da kuma jajircewarta wajen inganta harkokin Hajji da jin daɗin alhazai ‘yan Najeriya.
Ambasada Yusuf ya kuma nuna godiya ta musamman ga Mai Kula da Masallatan Harami Biyu da Gwamnatin Masarautar Saudiyya, musamman ga Ministan Hajji da Umrah, Dr. Tawfiq bin Fawzan Al-Rabiah, da Mataimakin Ministan Hajji da Umrah, Dr. Abdul Fattah bin Sulaiman Mashat, bisa ci gaba da haɗin kai da kuma wannan gagarumar kyakkyawar niyya da Masarautar ta nuna ga Najeriya da alhazanta.
Shugaban NAHCON ya bayyana cewa ƙarin guraben ya ƙara nuna kyakkyawar alaƙa da daɗaɗɗiyar dangantaka tsakanin Najeriya da Masarautar Saudiyya, tare da haɗin kan ƙasashen biyu wajen sauƙaƙa wa alhazan Najeriya gudanar da ibadar Hajji.
Ambasada Yusuf ya tabbatar da cewa za a gudanar da rabon ƙarin guraben cikin adalci, gaskiya da kuma bin ƙa’idoji, tare da cikakken bin dokoki da sharuddan gudanar da aikin Hajji na Najeriya da Saudiyya, cikin haɗin gwiwa da Hukumomin Jin Daɗin Alhazai na Jihohi da hukumomi da kwamitocinsu, da kuma kamfanonin jirgin yawo masu zaman kansu da ke da lasisi.
Shugaban NAHCON ya sake jaddada ƙudirin Hukumar na tabbatar da cewa Hajji ya kasance mai sauƙin samu kuma mai sauƙin kuɗi ga ‘yan Najeriya, tare da kiyaye ingancin ayyukan da ake samarwa, bin ƙa’idoji, tabbatar da gaskiya da riƙon amana, da kuma inganta yadda ake gudanar da ayyukan Hajji.
Ya kuma sake tabbatar da cewa Hukumar za ta ci gaba da aiki kafada da kafada da hukumomin da abin ya shafa a Masarautar Saudiyya da sauran masu ruwa da tsaki, domin tabbatar da ingantaccen shiri da gudanar da aikin Hajjin 2027, tare da kare mutunci, jin daɗi da kuma muradun alhazai ‘yan Najeriya.

