Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano ta cika alkawarin da ta dauka na samar da masauki mai kyau a kusa da Masallacin Harami (Masjid Al-Haram) da ke Makka, domin alhazai daga jihar Kano da za su gudanar da aikin Hajjin shekarar 2027.
A sanarwar da Jami’in hulda da jama’a na Hukumar, Sulaiman Abdullahi Dederi ya fitar, Daraktan Janar na hukumar, Alhaji Abubakar Ibrahim Matawalle, ne ya bayyana hakan a yau, yayin da yake jagorantar tawagar hukumar wajen duba gine-ginen masaukin da aka kulla yarjejeniyar amfani da su a kasar Saudiyya, a wani bangare na shirye-shiryen gudanar da aikin Hajjin 2027.
Wannan mataki na samar da masaukin na nuna irin kudirin hukumar na ganin alhazan jihar Kano sun samu masauki mai saukin isa, da jin dadi, tare da kusanci da wuraren ibada a tsawon zamansu na aikin Hajji.
Ya kuma bayyana cewa hukumar ta gudanar da jerin tarurruka da shugabancin Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON), da kuma hukumomin da abin ya shafa na kasar Saudiyya, domin tabbatar da nasarar gudanar da aikin Hajjin cikin sauki da tsari.
Alhaji Abubakar Ibrahim Matawalle ya bayyana gamsuwarsa kan yadda shirye-shiryen ke tafiya, tare da sake jaddada kudirin hukumar na samar da ingantaccen masauki da kyautata ayyukan jin dadin alhazai daga jihar Kano a lokacin aikin Hajjin 2027.
Ya kara da cewa hukumar za ta ci gaba da kokarin cika alkawuran da ta dauka, tare da daukar matakan da suka dace tun da wuri, domin tabbatar da gudanar da aikin Hajjin 2027 cikin sauki, kwanciyar hankali da nasara ga dukkan maniyyatan jihar Kano

