Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Sakkwato (SSPWA) ta bayar da tallafin kuɗi har naira miliyan bakwai da dubu ɗari shida da saba’in da biyu da ɗari takwas da ashirin da biyu (₦7,672,822) ga iyalan marigayi Malam Umar Faruku Suleiman, wanda aka fi sani da Mai Ruqiya, wanda kafin rasuwarsa ya kasance Mataimakin Shugaban Sashen Da’awah da Irshad na hukumar.
A sanarwar da Shugaban sashen yada labarai da sadarwa na Hukumar, Faruku Umar ya fitar, wata tawaga mai mambobi biyar da mahukuntan hukumar suka kafa domin gudanar da wannan aiki ce ta miƙa tallafin ga iyalan marigayin. Shugaban Sashen Da’awah da Irshad na hukumar, Sheikh Yahuza Shehu Tambuwal, ne ya jagoranci tawagar.
Wannan mataki na nuna irin kulawar da hukumar ke bai wa jin daɗin ma’aikatanta da iyalansu, tare da jajircewarta wajen girmamawa da yabawa gudummawar ma’aikatan da suka sadaukar da rayuwarsu wajen yi wa hukumar da al’ummar mahajjatan Jihar Sakkwato hidima.
Hukumar ta ci gaba da addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta wa marigayin kura-kuransa, Ya sanya shi cikin Aljannatul Firdaus, sannan Ya ba iyalansa haƙurin jure wannan babban rashi da ba ya da musaltuwa.

