Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Sokoto (PWA) ta fayyace cewa ba ta bude sabuwar rajista ga masu niyyar zuwa aikin Hajjin 2027 ba, bayan da Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta ware wa jihar karin kujerun aikin Hajjin.
A cewar Shugaban Sashen Yada Labarai da Sadarwa na Hukumar, Faruku Umar, Shugaban Hukumar, Alhaji Aliyu Musa, ya bayyana cewa an ware karin kujerun ne musamman domin masu niyyar zuwa Hajjin da suka riga suka biya kudin Hajji, amma ba su samu damar yin rajista ba saboda rashin wadatattun kujeru a lokacin rajistar.
Ya jaddada cewa karin kujerun ba na sabuwar rajista ko sabbin masu neman zuwa Hajji ba ne. An ware su ne domin samar da gurbi ga wadanda suka cancanta, wadanda tuni suka biya kudin Hajji amma suka kasa samun kujera sakamakon karancin adadin kujerun da aka bai wa jihar.
Don haka, Alhaji Aliyu Musa ya bukaci jama’a, musamman masu niyyar zuwa aikin Hajji, da su yi watsi da jita-jita da bayanan da ba a tantance ba da ke cewa Hukumar ta fara sabuwar rajistar Hajjin 2027.
Ya shawarci masu niyyar zuwa Hajji da su rika dogaro da sanarwar hukuma daga Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Sokoto da kuma NAHCON domin samun sahihan bayanai game da shirye-shiryen Hajjin 2027.
Shugaban Hukumar ya tabbatar wa jama’a cewa Hukumar za ta ci gaba da kokarinta na tabbatar da gudanar da aikin Hajji cikin gaskiya, tsari da sahihanci, tare da gode wa masu niyyar zuwa Hajjin bisa hadin kai da fahimtar da suke nunawa.

