Shugaban HIN, Farfesa Nasiru Maiturare, tare da mataimakinsa, Farfesa Wasiu Gabadeen, sun kai ziyarar girmamawa ga Darakta Janar na IsDBI, Dakta Sami Al-Suwailem, domin tattauna hanyoyin kafa haɗin gwiwa a fannonin gudanar da bincike na bai ɗaya, horar da ƙwararru, haɓaka ƙwarewar ma’aikata da hukumomi, da kuma samar da sabbin dabaru wajen inganta harkokin aikin Hajji da Umrah.
A yayin ganawar, Cibiyar IsDBI ta bayyana aniyarta ta tallafa wa HIN ta fuskar haɗin gwiwar bincike da kuma yiwuwar bayar da tallafin kuɗi, musamman a fannin binciken da ya shafi tattalin arzikin aikin Hajji.
Haka kuma, cibiyar ta yi alƙawarin bayar da tallafin fasaha wajen samar da tsarin koyarwa ta yanar gizo (E-learning), domin sauƙaƙa gudanar da shirye-shiryen horar da masu ruwa da tsaki a harkokin Hajji da Umrah, tare da faɗaɗa damar samun ilimin ƙwarewa ga masu aiki a wannan fanni.
A wani mataki na nuna kyakkyawar alaƙa, IsDBI ta bai wa HIN gudummawar ɗaruruwan littattafai da wasu muhimman wallafe-wallafen ilimi, waɗanda za su taimaka wajen bunƙasa ɗakin karatu da albarkatun bincike na cibiyar.
Sauran waɗanda suka halarci taron daga tawagar IsDBI sun haɗa da Mista Sharjeel Ahmad, ƙwararre kan koyarwa ta yanar gizo, da Dakta Habeeb Idris Pindiga, Mataimakin Manaja a ƙungiyar Knowledge Horizons.
Wannan ganawa na zama wani muhimmin ci gaba mai ƙarfafa gwiwa a ƙoƙarin HIN na amfani da ƙwarewa da gogewar ƙasashen duniya wajen inganta bincike, ƙarfafa ƙwarewar cibiyar da kuma hanzarta sauya tsarin koyar da harkokin Hajji da Umrah zuwa na zamani a Najeriya.
Ana sa ran wannan haɗin gwiwa zai taka muhimmiyar rawa wajen inganta ƙwarewar ma’aikata, ingancin gudanarwa da kuma samar da ci gaba mai ɗorewa a harkokin Hajji da Umrah a Najeriya.

