Ministan Hajji da Umrah na Saudiyya, Tawfiq Al-Rabiah, ya kai ziyarar duba yadda aka shirya sansanonin Mina domin tantance matakin kammala shirye-shiryen Hajjin shekarar 2026.
Ziyarar na daga cikin rangadin duba shirye-shiryen da ake yi a fili domin tabbatar da cewa kayayyaki da ayyukan hidima sun kai matakin da ake bukata kafin isowar alhazai. A cewar ministan, an fara shirye-shiryen hajjin tun da wuri, wanda hakan ya taimaka wajen inganta shirye-shiryen sansanonin da kuma kara ingancin gudanar da ayyuka ta hanyar hadin gwiwar hukumomin da abin ya shafa.
Al-Rabiah ya bayyana cewa an samar da sabbin tsarin na’urorin lantarki domin bibiyar motsin alhazai tare da tsara yadda ake shiga da fita daga sansanonin. Ya kuma kara da cewa an girke alamomi a muhimman hanyoyin shiga da fita, wadanda ke nuna lokutan fita da dawowa da kuma sauran muhimman umarni.
Ya ce wadannan matakai na taimakawa wajen inganta sarrafa cunkoso da kara tabbatar da tsaron alhazai, wanda ya yi daidai da kokarin ma’aikatar na cimma manufofin Saudi Vision 2030 da kuma Shirin Inganta Kwarewar Alhazai (Pilgrim Experience Program).

