Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta nemi kara karfafa hadin gwiwa da Rundunar ’Yan Sandan Najeriya domin inganta harkokin tsaro da tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin maniyyatan aikin Hajji a lokacin gudanar da aikin Hajji.
A sanarwar da Jami’in hulda da jama’a na Hukumar, Habibu Yusuf Babura ya fitar, Daraktan-Janar na Hukumar, Alhaji Ahmad Umar Labbo, FCFA, NFI, ne ya bayyana hakan a lokacin da ya jagoranci tawagar hukumar zuwa hedikwatar Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta Jihar Jigawa domin kai ziyarar ban-girma.
Ya ce ziyarar ta kasance wani bangare na kokarin karfafa alakar aiki tsakanin hukumar da rundunar ’yan sanda, musamman a fannonin tsaro, sadarwa, musayar bayanai da hadin gwiwa tsakanin hukumomin gwamnati.
Alhaji Labbo ya jaddada muhimmancin samar da ingantattun tsare-tsaren tsaro domin kare maniyyata, jami’ai da sauran masu ruwa da tsaki a duk tsawon lokacin gudanar da aikin Hajji.
Daraktan-Janar din ya kuma nuna godiya ga Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Jigawa, CP Tijjani Murtala, bisa karbar tawagar da kuma irin goyon baya da hadin gwiwar da Rundunar ’Yan Sandan Jihar ke ci gaba da bai wa hukumar.
Da yake mayar da jawabi, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Jigawa, CP Tijjani Murtala, ya yaba da wannan ziyara, tare da jinjina wa Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa bisa muhimmiyar rawar da take takawa wajen kula da jin dadin alhazai da taimaka musu wajen gudanar da ibadunsu.
CP Murtala ya tabbatar wa tawagar hukumar cewa Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa a shirye take ta ci gaba da yin aiki kafada da kafada da hukumar da sauran hukumomin da abin ya shafa domin tabbatar da tsaro da walwalar maniyyata da jami’an da za su gudanar da aikin Hajji.
Ya ce rundunar za ta ci gaba da samar da ingantaccen tsaro na kwarewa, mai saurin daukar mataki da kuma dogaro da bayanan sirri a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.
Kwamishinan ya kara jaddada muhimmancin fara shirye-shiryen tsaro tun da wuri, musayar bayanai da kuma tsara ayyukan tsaro cikin hadin gwiwa, yana mai cewa hadin kan hukumomin da abin ya shafa na da matukar muhimmanci wajen samun nasarar gudanar da aikin Hajji cikin tsari, aminci da kwanciyar hankali.
Taron ya kammala cikin yanayi mai kyau, inda bangarorin biyu suka sake tabbatar da aniyarsu ta ci gaba da hadin gwiwa, taimakon juna da ingantaccen tsarin aiki domin kare lafiyar jama’a da tabbatar da jin dadin alhazai daga Jihar Jigawa.

