Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) da Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zariya, sun rattaba hannu kan Yarjejeniyar Haɗin Gwiwa (MoU) domin ƙaddamar da shirin Master of Business Administration (MBA) a Fannin Gudanar da Ayyukan Hajji (Hajj Operations Management). An sanya hannu kan yarjejeniyar ne a ranar Jumma’a, 31 ga Yuli, 2026, a hedikwatar NAHCON da ke Abuja.
A sanarwar da Hukumar NAHCON ta fitar, Shugaban Hukumar NAHCON, Ambasada Isma’il Abba Yusuf, tare da Sakataren Hukumar, Dr. Mustapha Muhammad Ali, ne suka sanya hannu a madadin NAHCON. Daga bangaren Jami’ar ABU kuwa, Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Adamu Ahmed, da Magatakardar Jami’ar, Malam Rabiu Samaila, su ne suka sanya hannu.
A jawabinsa, Ambasada Isma’il Abba Yusuf ya bayyana wannan haɗin gwiwa a matsayin wani babban ci gaba wajen ƙwarewa da inganta harkokin Hajji da Umrah a Najeriya. Ya ce gudanar da ayyukan Hajji na ƙara zama masu sarkakiya, don haka akwai buƙatar ƙwararrun ma’aikata masu ilimi na musamman, ƙwarewar aiki da cikakkiyar fahimta game da yadda harkokin aikin Hajji ke sauyawa a duniya. Ya ƙara da cewa sabon shirin zai haɗa ingantaccen ilimin jami’a da kuma horo na aikace domin inganta tsare-tsare, daidaitawa da kuma ingancin ayyukan hidima ga alhazai.
Shi ma Mataimakin Shugaban Jami’ar ABU, Farfesa Adamu Ahmed, ya bayyana cewa wannan shiri ya samo asali ne daga kusan shekaru goma na tattaunawa da haɗin gwiwa tsakanin jami’ar da NAHCON. Ya ce shirin zai haɗa ilimin jami’a mai inganci da ƙwarewar aiki domin samar da ƙwararru masu ilimi da basirar da ake buƙata wajen tafiyar da harkokin Hajji da Umrah yadda ya dace da sauye-sauyen zamani.
Tawagar Jami’ar ABU ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Jami’ar ta haɗa da Farfesa Mohammed Bashir Mu’azu, Daraktan Cibiyar Koyo Daga gida ta ABU; Malam Rabiu Samaila, Magatakardar Jami’ar; Farfesa Sanusi Aliyu Rafindadi, Mataimakin Shugaban Jami’a mai kula da Ci gaba, Bincike da Ƙirƙire-ƙirƙire; Farfesa Auwalu Haruna, Daraktan Cibiyar Tattalin Arziki da Kuɗi ta Babban Bankin Najeriya (CBN Centre for Economics and Finance); tare da sauran manyan jami’an jami’ar.
A ɓangaren NAHCON kuwa, tawagar ta kasance ƙarƙashin jagorancin Shugaban Hukumar kuma Babban Jami’in Gudanarwa, tare da Sakataren Hukumar, Daraktoci, Shugaban Cibiyar Horar da Ma’aikatan Hajji ta Najeriya (Hajj Institute of Nigeria – HIN), Farfesa Nasiru Maiturare, da sauran manyan jami’an gudanarwa.
Shirin na MBA haɗin gwiwa ne tsakanin Hajj Institute of Nigeria (HIN) da Cibiyar Koyo daga Gida ta Jami’ar ABU.
Za a buɗe damar shiga shirin ga ma’aikatan NAHCON, Hukumomin Jin Daɗin Alhazai na Jihohi, kamfanonin Hajji da Umrah masu lasisi, ƙwararru a fannin tafiye-tafiye, Jirgin Yawo da baƙunci, malamai, ‘yan kasuwa, da kuma masu neman gina sana’a a harkokin gudanar da Hajji a Najeriya da ma duniya baki ɗaya.
NAHCON ta bayyana cewa wannan shiri na farko irinsa zai taimaka wajen ɗaga ƙa’idodin ƙwarewa, inganta ayyukan da ake yi wa alhazai, tare da ɗaga martabar Najeriya a matsayin cibiyar duniya ta ilimi, horo da bincike kan harkokin Hajji.
Saboda haka, Hukumar ta ƙarfafa duk masu cancanta da sauran masu sha’awa su yi anfani da wannan dama ta musamman.
Za a sanar da ƙarin bayani kan sharuɗɗan shiga, hanyoyin neman gurbin karatu da kuma ranar fara shirin daga Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya, nan gaba kaɗan.

